Mun yi amfani da garken kuri’u amma domin gwajin somin-tabi – Inji INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta ce ta yi amfani da na’urorin zamani wajen tattara kuri’un zaben shugaban kasa da aka yi a bana. Wannan batu ya dade ya na jawo magana.
Kwamishinan hukumar zabe na INEC na yankin Kogi, Kwara da jihar Nasarawa, watau Malam Mohammed Haruna, wanda ya wakilci shugaban INEC na kasa, a wajen wani taro, ya bayyana wannan.
Daily Trust ta rahoto Jami’in na INEC ya na cewa: “Abin la’akari shi ne, gwaji kurum mu ka yi. Mun duba yiwuwar amfani da na’urorin zamani ne kawai a zaben 2019 domin har yanzu bai shiga doka ba.”
Mohammed Haruna da ya ke jawabinsa a wajen wani taro da kungiyar YIAGA ta shirya game da zaben Najeriya na 2019 ya ce: “A doka, INEC ba ta damar amfani da na’ura wajen tura sakamakon zabe.”
Haruna a madadin Farfesa Mahmood Yakubu, ya kara da cewa: “Kamar yadda YIAGA ta fada, da shugaban kasa ya sa wannan a kudirin zabe, da mun samu damar hankada kuri’u ta na’urorin zamani.”
KU KARANTA: Jigon APC a Najeriya ya ce za su yi nasara a wasu zabukan bana
“Hatta sabon kudirin zaben da aka kai gaban shugaban kasa bai dauke da batun amfani da uwar-garke wajen tattara sakamakon zabe. Kamar yadda na fada, har yanzu babu wannan doka.” Inji Haruna.
Malam Haruna wanda ya kuma wakilci jami'in INEC, Festus Okoye a taron, ya na cewa: “Yanzu mu na jarraba wadannan na’urori ne a jihohi, ko a zaben shugaban kasa, gwaji ne kurum mu ka soma.”
Babban jami’in na INEC ya kuma nuna cewa dole su bi a hankali wajen aiki da na’urorin zamani domin ana iya yi masu kutse a zabe. An shirya wannan taro ne jiya 31 ga Agusta a babban Birnin Abuja.
'Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya a zaben bana, ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben 2019 kamar yadda kuri'un da ke cikin garken INEC ya nuna.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng