Tirkashi: 'Yan sandan Najeriya tarin dakikai ne da marasa hankali - P-Square

Tirkashi: 'Yan sandan Najeriya tarin dakikai ne da marasa hankali - P-Square

- Daya daga cikin fitattun mawakan nan na P-Square, wanda ake kira da Paul Okoye ya caccaki jami'an 'yan sandan Najeriya

- Mawakin ya bayyana cewa a lokacin da duk wani matashi mai abin yi yake kokarin ganin ya mayar da kasarsa abin alfahari a idon duniya, su kuma 'yan sanda basu da aiki sai bawa mutane kunya

- Mawakin ya bayyana bacin ran nasa ne saboda wani hari da aka kai wa wata dalibar jami'ar FUTA da kuma wani dan wasan kwallon kafa

Daya daga cikin fitattun mawakan kudancin Najeriyan nan wadanda tauraruwarsu ta haska a shekarun da suka gabata, P-Square, mai suna Paul Okoye ya caccaki jami'an hukumar 'yan sandan kasar nan.

Paul bai ji dadin abinda 'yan sanda suke yi ba akan harin da aka kaiwa wata dalibar jami'a ta FUTA da kuma dan wasan kwallon kafa.

Wannan dalili ne yasa ya wallafa wata magana a shafinsa na Instagram inda ya ya yiwa jami'an hukumar 'yan sandan kaca-kaca.

KU KARANTA: Tirkashi Orubebe yayi kashi mai wari: Baza mu taba bari Orubebe ya dawo jam'iyyar mu ba - APC

Mawakin ya ce: "A lokacin da mawaka, jarumai, 'yan wasa da kuma kananan 'yan kasuwa suke iya bakin kokarinsu domin ganin sun mayar da kasarsu abin alfahari a idon duniya, a lokacin ne su kuma 'yan sandan Najeriya suke bamu kunya, tarin dakikai da mahaukata kawai."

Ya kara da cewa: "'Yan sandan Najeriya tarin dakikai ne da marasa hanakali, wannan babban abin kunya ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng