Barayin mutane sun kashe mutane 3, sun yi garkuwa da wasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Barayin mutane sun kashe mutane 3, sun yi garkuwa da wasu a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Wasu gungun miyagun yan bindiga sun sake komawa babbar hanyar Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 26 ga watan Agusta, inda suka kashe mutane uku, tare da yin awon gaba da wasu da ba’a san adadinsu ba.

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 5:30 na yamma, kamar yadda wani direba da abin ya faru a gabansa, kuma ya sha da kyar ya tabbatar, wanda ya bayyana cewa da idanunsa ya ga gawarwakin.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Yan bindiga sun yi awon gaba da Mata da yan mata 46 a Katsina

Majiyar Legit.ng ta ruwaito direban mai suna Jibrin Adamu ya bayyana cewa da misalin karfe 5:30 na yammacin Litinin, 26 ga watan Agusta ne yan bindigan suka tare hanyar, inda suka bude wuta a kan motocin dake tafiya a kan hanyar a wannan lokaci, a dalilin haka suka kashe mutane 3, suka tafi da wasu fasinjoji da dama cikn daji.

“Da idanu na na ga gawarwakin mutane uku a gefen hanya, da kuma motoci guda 6 wadanda duk sun kwashe fasinjojin cikinsu, amma daga bisani yan bindigan sun tsere a lokacin da Sojoji suka isa wajen bayan kwashe kimanin mintuna 30 suna cin karensu babu babbaka.” Inji Jibrin.

Shima wani direban da lamarin ya faru a idonsa, Danladi Sani yace: “Da kyar na tsallake rijiya da baya ni ma a daidai kamfanin Olams, saboda mota ta na bayan wata motar da yan bindigan suka bude ma wuta, da kyar na juya da baya na koma shingen binciken ababen hawa na Sojoji.

“Daga cikin motocin da naga sun kwashe fasinjojin cikinsu akwai wata motar Tirela, sa’annan na ga gawarwaki har guda uku a kwance cikin jini a gefen hanya.” Inji shi.

Sai dai ko da majiyarmu ta tuntubi kaakakin Yansandan jahar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, don jin ta bakinsa game da lamarin, sai ya nemi ta bashi lokaci ya tabbatara kafin ya yi wani magana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel