Da'u Fataken Dare: Cikin minti hudu kacal muke sace kwakwalwar kowacce irin mota - Wasu manyan barayi

Da'u Fataken Dare: Cikin minti hudu kacal muke sace kwakwalwar kowacce irin mota - Wasu manyan barayi

- Wasu barayi da suka kware wajen satar 'brain box' na mota sun bayyana yawan lokacin da suke dauka wajen kwance 'brain box' din daga jikin mota

- Barayin sun bayyana cewa mintuna hudu kacal suke yi su raba mota da kwakwalwar ta

- Sun kuma bayyana cewa suna zuwa satar ne a wuraren holewa da misalin karfe 1 zuwa 2 na dare, a lokacin da mutanen dake wajen sun bugu da giya

Rundunar 'yan sandan RRS dake jihar Legas sun samu nasarar kama wasu manyan barayi guda biyu da suka kware matuka wajen kwance kundun kwakwalwar mota, wanda aka fi sani da 'Brain Box' cikin miniti hudu kacal.

An kama Sodiq Musa mai shekaru 28 da kuma Sa'idu Atiku mai shekaru 34, dauke da wata akwatu wacce suka dauko kwakwalwar motar guda uku.

Wani abokin harkar ta su mai suna Ridwan Adamu ya gudu dauke da kwakwalwar guda daya a hannunshi. Hakan yake nuna sun sato kwakwalwar guda hudu ne.

Daya daga cikin barayin mai suna Musa ya bayyana cewa ya kammala karatunsa na digirin farko a jami'a, inda a shekarar 2017 ya nufi jihar Legas domin neman kudi.

"Muna amfani da wani dutse ne sai mu raba wutar fulogi saboda kada aji karar motar, cikin mintuna biyu kacal sun isa mu kwance 'brain box' na Toyota Hiace, sannan kuma idan Toyota Hilux ce bai wuce mintuna hudu."

KU KARANTA: Mai kudi ma kenan, bare talaka: Bani da gida ko daya a kasar waje, saboda bana rayuwa mai tsada - Aliko Dangote

Haka Musa ya bayyana wanda Ridwan kafin ya shigar da shi hanyar sata, ya taba aikin gasa nama a wani otal

Ya ci gaba da shaida wa jami’an RRS cewa a baya can Atiku mai gadi ne a wani kamfani da ke kan titin da aka kamo su. Shi ne ya kira shi domin su sace ‘brain boxes’ na wasu motocin kamfanin.

Sun shaida wa jami’an tsaro cewa ‘brain box na Hilux ya na da tsada, domin ya na kai har naira 40,000.

"Sannan muna sayarwa mutane ne a wajen kasuwa saboda basa yarda su shigo cikin kasuwa, duka cinikin muna gama shi a cikin mintuna biyu ne fah, mu basu 'brain box' su bamu kudi kowa ya kama gabanshi.

"Ridwan ne yake bani kashi 40 bisa 100 na kudin da muka samu. Sannan mun fi yin satar a wuraren holewa da misalin karfe 1 ko 2 na dare a daidai lokacin da yawancin mutanen dake wajen sun sha giya sunyi mankas."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng