Amfanin ridi guda 10 a jikin Dan Adam
Al’umman kasar Najeriya na noman ridi sosai sannan kuma mutane na sarrafa tare da amfani da shi wajen yin abubuwa da dama musamman wajen yin abinci da sauran su.
Da dama na da masaniya game da ridi sai dai yadda suke amfani da ita ne ya banbanta.
Ana amfani da ridi wajen ci haka kawai da siga ko kuma da gishiri. Wasu kan hada shi don maganin bakon dauro a yara sannan kuma wasu kan markada sannan su cire man shi don amfani da shi a abinci, man kai da na jiki da dai sauransu.
Likitoci sun yi kira ga mutane da su rika cin ridi don amfanin da yake da shi a jikin mutum.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan Shi’a sun toshe mashigin majalisar dokokin kasar
Ga wasu daga cikin amfanin ridin:
1. Ridi na rage cutar siga.
2. Ridi na taimaka wa masu fama da ciwon ido.
3. Ridi na taimakawa wajen nika abinci a cikin mutum.
4. Yana rage kiba a jiki.
5. Yana kuma kawar da cututtukan dake kama zuciya.
6. Ridi na maganin Asma.
7. Ridi na dauke da sinadarin Iron dake taimakawa wajen kawar da cututtukan dake kama jini.
8. Yana dauke sinadarin Folic Acid dake taimakawa mata masu ciki da dan dake cikin su.
9. Ridi na karfafa karfin kashi.
10. Yana kawar da cututtukan dake kama fata kamar su kuraje kuma yana hana tsufa da wuri.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng