Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda a Enugu

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda a Enugu

Wasu yan bindiga a ranar Lahadi, 25 ga watan Agusta, sun kai hari ofishin yan sanda na Ikirike a jihar Enugu.

Kakakin yan sandan jihar, Ebere Amaraizu, wanda ya tabbatar da afkuwar al’amarin, ya bayyana cewa sun zo ne a siga na mutanen da ke cikin wani mawuyacin hali sannan suka kaddamar da harin.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, babu bayani kan ko an rasa rai a harin.

A wani labarin kuma, mun ji cewa mahukunta a kasar Nijar sun ce wasu 'yan ta'adda da ake zargin mayakan kungiyar masu tayar da kayar baya na Boko Haram ne sun hallaka mutane 12 a garin Gueskerou na jihar Diffa wanda ke iyaka da kasar Najeriya.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne mahara haye a kan babura, suka kai hari kauyen Lumana a yankin garin Gueskerou kamar yadda mazaunansa suka shaidawa manema labarai na BBC Hausa.

KU KARANTA KUMA: Kaftin Tijjani Balarabe: Ku sadu da jami'in sojan da ya ubutar da Wadume daga hannun 'yan sanda

Bayan razanar da al'ummar garin ta hanyar harbe-harben harsashin bindiga saman iska, maharan sun kuma hallaka mutane 12 ta hanyar yankan rago da wukake, inda suka fice salin alin a sanadiyar rashin jami'an tsaro da za su mai da martani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel