Da dumi-dumi: Shugaba Buhari ya ziyarci sansanin Batsari a Katsina
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 14 ga watan Agusta, ya ziyarci karamar hukumar Batsari domin yin jaje ga yan gudun hijira a yankin.
Batsari na daya daga cikin kananan hukumomi takwas da suka fuskanci hare-haren yan bindiga da kuma garkuwa da mutane a jihar Katsina.
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ne ya tarbi Shugaban kasar.
Gwamnan a ciki jawabinsa yace tura karin jami’an tsaro da kayayyaki da aka yi zuwa wannan yanki a kwanan nan ya taimaka matuka wajen rage yawan hare-hare.
Ya kuma yarda cewa har yanzu akwai lamarin hare-hare, garkuwa da mutane da kuma fashin shanu a yankin.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar tare da taimakon sauran hukumomin tsaro tayi nasarar shawo kan wannan lamari ta hanyar tattaunawa da kuma shirinta na afuwa.
KU KARANTA KUMA: El-Zakzaky: Likitoci 186 daga kasashe 7 sun rubuta wa Buhari wasika (karanta)
A wani labarin kuma mun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kashe dan shugaban mafarauta na Bunu, Caleb Oshe da dansa mai suna Sunday a garin Suku da ke karamar hukumar Kabba-Bunu na jihar Kogi.
Daily Trust ta ruwaito cewa wasu mutane dauke da bindigu sun kai hari gidan shugaban mafarautan wadda shine kuma shugaban 'yan kungiyar tsaro na sa kai a garin misalin karfe 3 na daren jiya Talata.
Daga bisani an gano cewa 'yan bindigan sun nemi a basu kudi sannan suka sace wasu kayayaki masu daraja.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng