Ronaldo ya bayyana babban banbancinsa da Tauraro Lionel Messi

Ronaldo ya bayyana babban banbancinsa da Tauraro Lionel Messi

- Cristiano Ronaldo ya jinjinawa kansa wajen kamantasa da a ke yi da Lionel Messi

- Babban ‘Dan kwallon na Duniya ya ce ya zagaya kungiyoyi da dama ya dauki kofi

Babban ‘Dan kwallon kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya yi magana game da babban Abokin hamayyarsa Lionel Messi, inda ya ce banbancinsa da ‘Dan wasan na Barcelona shi ne, shi ya zagaya Duniya.

Cristiano Ronaldo ya ke cewa shi ya buga wasa a kungiyoyi da dama inda ya kuma yi nasarar lashe gasa iri-iri; daga cikin har da babban kofin Nahiyar Turai. Ronaldo ya daga wannan kofi sau biyar a rayuwarsa.

‘Dan wasa Ronaldo ya fara kwallo ne a Sporting Lispon, inda daga bayan ya koma Manchester United inda ya fara cin kofi. A 2009 kuma ya dawo Real Madrid, ya lashe Gasar kofin Turai sau 4 a kulob din.

KU KARANTA: An dakatar da 'Dan wasan Argentina Lionel Messi daga buga kwallo

Yanzu Ronaldo ya na taka leda ne a Juventus inda ya ci kofi bayan zuwansa bara. ‘Dan wasa Ronaldo ya ke cewa: “Ba kasafai a ke samun ‘yan kwallon da ka su dauki kofin Gasar Turai sau biyar ba.”

A wani shiri da a ke yi a kan babban ‘Dan wasan, Cristiano Ronaldo ya na cewa “Ni ne na yi shekaru shida a jere i na zama wanda ya fi kowa zura kwallaye mafi yawa a Gasar cin kofin Nahiyar Turai.

“Messi babban ‘dan wasa ne wanda bayan ya yi nasarar samun Ballon d’Or birjik, duk shekara kamar ni, ya na kara kwarewa a Duniya.” Sai dai kuma Messi bai taba barin kungiyarsa ta Barcelona ba.

Ronaldo ya ce: “Duk rana i na tashi ne da shirin cigaba da koyon kwallo da niyyar ganin na samu wasu nasarorin, Ba kudi ba kurum. “Na godewa Allah, ba ni da matsalar kudi, abin da na ke so shi ne in bar tarihi a kwallo.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel