Zaben Kogi: Dangin Marigayi Abubakar Audu su na harin tikitin APC

Zaben Kogi: Dangin Marigayi Abubakar Audu su na harin tikitin APC

Mun samu rahoto cewa bisa dukkan alamu za a fafata tsakanin wasu daga cikin dangin Prince Abubakar Audu su na neman tikitin takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin jam’iyyar APC.

Iyalan Marigayi tsohon gwamna Prince Abubakar Audu za su kara da junansu ne wajen samun tutan takara a jam’iyyar APC a zaben fitar da gwani da za a yi a karshen watan Agustan nan.

Hakan na zuwa ne bayan da Dangin tsohon gwamnan su ka gaza tsaida mutum daya a cikinsu da zai kara da gwamna mai-ci watau Yahaya Bello. Za a yi babban zaben jihar ne a Watan Nuwamba.

Daily Trust ta rahoto cewa masu neman tikitin APC a zaben gwamnan na Kogi sun hada da babban Yaron Marigayi Gwamna Audu; Mohammed Audu da kuma ‘Danuwansa Mustapha Mona.

KU KARANTA: Gwamna da Kwamishinansa za su amsa kara a gaban kuliya a Ekiti

Haka zalika Prince Yahaya Audu, wanda ‘Danuwa ne wurin Marigayin ya na cikin masu harin kujerar gwamna Bello. Tuni dai Prince Audu da da Mona Audu sun yanki fam din takara a bana.

Rahotanni sun bayyana cewa a na saida fam din nuna sha’awar tsayawa takarar gwamnan Kogi a jam’iyyar APC ne a kan kudi Naira miliyan 22.5. Mohammed Audu ne kurum bai saye fam ba.

Alamu na nuna cewa Mohammed Audu zai yi wuf ya saye na shi fam din takarar kafin APC ta rufe saidawa. A gidan tsohon gwamnan kurum APC ta samu kusan Naira miliyan 70 kafin zabe.

Daga cikin sauran wadanda za su kalubalanci tazarcen gwamna Yahaya Bello a APC wannan karo akwai; Seidu Mohammed Ogah; Alhaji Sani Lulu Abdullahi da kuma Vice Admiral Jibrin Usman.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel