Na fi jin dadin aikin hajji cikin talakawa – Gwamnan jihar Bauchi

Na fi jin dadin aikin hajji cikin talakawa – Gwamnan jihar Bauchi

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi, ya ce shi da wasu mukarrabansa da suke aikin hajjin suna zaune ne a gidan alhazai na gama-gari daga jihar, maimakon kasaitaccen masauki ko otal.

A cewar gwamnan shiga cikin talakawa a lokacin aikin hajji ya fi dadi da lada, kuma ta hakan zai san matsalolin alhazan domin magance su.

Shafin BBC ta ruwaito cewa a wata hira da tayi da gwamnan daga kasar Saudiyya, ya ce zama cikin alhazai talakawa shi ne mafi alheri a wurinsa maimakon kebe kansa a wani masauki na kasaita.

Gwamnan ya ce a baya yakan je aikin hajjin ne ya kasance cikin tawaga ta manya da kan sauka a manya-manyan otal na kasaita irin su Hilton, ba ya shiga cikin alhazai gama-gari da kan zauna a masauki irin su Masfala, a yi tafiya ta kusan kilomita 4 zuwa 5 a kasa, kafa na ciwo, kuma ana ganin yadda kowa yake fama.

KU KARANTA KUMA: Hotunan Aisha Buhari da matan shugabannin kasashen Afirka a kasa mai tsarki

Amma yanzu sai ya yanke shawara ya shiga cikin sauran alhazai da kan cakudu da juna, tun bayan da a wata shekara a baya ya yi irin wannan cakuduwa har ma ya zama jagoran tawagarsu a motar da suka shiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel