Matashi ya samu kyautar wayar Salula kirar 'Iphone' kwana daya bayan siyar da wayarsa domin siyen Dabbar Layya a Jigawa

Matashi ya samu kyautar wayar Salula kirar 'Iphone' kwana daya bayan siyar da wayarsa domin siyen Dabbar Layya a Jigawa

Wani matashi dan Jigawa mai suna, Isma'eel S Jauro, ya samu kyautar waya Salula kirar 'Iphone' kwana daya bayan siyar da wayarsa domin siyen Dabbar Layya

Biyo bayan amfani da hudubar da wani malamin addinin musulunci ya gabatar a yayin sallar Juma'a akan irin muhimmanci da kuma falala dake tattare da yin layya.

Matashi Isma'eel S Jauro ya wallafa a shafin sa na sada zumunta cewa, ya siyar da babbar wayar salular sa domin siyen dabbar layya domin kasancewa daga cikin wadanda za su amfana da falalar dake tattare da yin layya.

Kwatsam matashin ya wayi safiya da samun sakon waya kirar Iphone S4 daga wani mutum, abin da ya sanya shi kasa boye farin cikin sa kan lamarin.

Yace: "Bayan da na bayyana cewa a jiya na sayarda wayata domin sayen dabbar layyah sanadin hudubar da naji a masallacin Jum'a dana halatta jiya. Kwatsam yau din nan da sanyin asubahi sa ga shi wani mai kaunata ya aikomin da wayar Iphone 4s.

Ina godewa Allah bisa ni'ima da yake mana da hadamu da mutanen kirki masu kaunarmu, na go de da wannan kyautar da akayimin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel