Mahajjatan Najeriya 6 sun rasu a kasar Saudiyya

Mahajjatan Najeriya 6 sun rasu a kasar Saudiyya

Hukumar da ke kula da jin dadin Mahajjatan Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa maniyyatan kasar shida ne suka rasu a kasar Saudiyya.

Kwamishinan gudanarwa na hukumar Abdullahi Modibbo Saleh ya bayyana cewa duka mahajjatan da suka rasu "lokacin su ne ya yi."

Har ila yau ya ce kimanin mutane 45,000 ne suka isa kasar don gudanar da aikin Hajjin bana, wadda ake sa ran akalla mutum miliyan biyu daga sassan duniya daban-daban za su gudanar da aikin, wanda shi ne taron jama'a mafi girma a duniya.

Ya kuma ce akwai kimanin mahajjata 300 daga jihar Kano da ba za su samu damar yin aikin hajji ba saboda matsalolin sufuri.

A ranar Asabar, 9 ga watan Dhul Hijjah, 1440 BH ne za a yi hawan Arfa, mafi muhimmanci a aikin Hajji.

KU KARANTA KUMA: Kalli wani Alhaji yana dawafi dauke da mahaifiyarsa a wuyarsa

A wani labarin kuma, Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta karrama wasu Musulmai yan Najeriya guda biyu da suka nuna kyawawan halaye abin koyi, a yayin aikin Hajji na bana.

Legit.ng ta ruwaito wadannan mutane biyu sun hada ne da Imam Abubakar Abdullahi, limamin wani Masallaci dake jahar Filato wanda ya ceci wasu kiristoci yan kabilar Berom fiye da 300 daga harin yan bindiga, da kuma Kofur Bashir Umar, Sojan daya tsinci N15,000,000 kuma ya mayar.

Hukumar NAHCON ta karrama Imam Abubakar ne ta hanyar sanyashi cikin tawagar Malaman Hajji ta kasa da zasu gudanar da wa’azuzzuka da tunatarwa ga mahajjatan Najeriya a yayin aikin Hajji.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel