Cikin Hotuna: Gbajabiamila ya gamu da Aisha Buhari a Makkah
A halin yanzu, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, tare da kakakin majalisar wakilai na Najeriya, Femi Gbajabiamila, su na kasa mai tsarki domin sauke farali na aikin Hajji a bana.
A watan Mayun da ya gabata, Aisha ta kasance a kasar ta Saudiya wajen gudanar da aikin Umara tare da mai gidanta shugaba Buhari.
Wasu hotunan kakakin majalisar wakilai na Najeriya da kuma uwargidan shugaban kasa Buhari sun bayyana a ranar Juma'a.
Legit.ng ta fahimci cewa, Gbajabiamila shi ne ya yada wannan hotuna a shafinsa na sada zumunta na Twitter da safiyar Juma'a, 9 ga watan Agustan 2019.
KARANTA KUMA: Manoman Tumatir a Kano na asarar kaso 40% na amfanin gona a duk shekara
Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng