Kada ku siyasantar da aikin hajji – Sheikh Al Sudais ga mahajjata

Kada ku siyasantar da aikin hajji – Sheikh Al Sudais ga mahajjata

Babban malamin nan na kasar Saudiyya, Sheikh Abdul Rahman Al Sudais, ya bukaci mahajjata da su kiyayi ayyukan da ka iya siyasantar da aikin Hajjin.

Al-Sudais ya bayyana aikin Hajji a matsayin “sakon zaman lafiya”, ya kuma bukaci bayin Allah da su guje ma duk wani aiki da zai siyasantar da aikinsu.

Yace musulunci ya yi hani ga tsatsauran ra'ayi, ta’addanci da kuma barna, inda ya bukaci mahajjatan da su yi amfani da lokutansu wajen sanin juna domin amfani da kuma jin dadin kowa.

Yayinda yake zantawa da tawagar manema labarai na kasa da kasa wadanda ministan labarai na kasar Saudiyya ya gayyara a Makkah, a ranar Talata, Sudais wanda ya kasance babban jigon da ke kula da harkokin tsarkakan masallatan kasar guda biyu, yace kasar Saudiyya ta kasance alama da ke nuni ga gyara da kuma wanzar da zaman lafiya

Ya bukaci kafofin sadarwa da su samar da sanayya tsakanin kasashen musulunci dangane da al’amuran da ke faruwa ga al’umman musulmai.

KU KARANTA KUMA: Hajjin Bana: Bamu karbi kudin hadayar maniyyatan Kano ba - Hukumar Alhazai

Ya kuma yabi kafofin sadarwa akan kasancewarsu amintattu wajen yada ma duniya labarai, sannan ya bukace su da su zamo masu fada ma mutane gaskiya sannan kuma su guji yi wa Musulunci mummunan fasara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel