WAEC: Za mu koma gudanar da jarrabawa da gafaka a nan gaba

WAEC: Za mu koma gudanar da jarrabawa da gafaka a nan gaba

Shugaban hukumar jarrabawar kamalla Sakandare na yankin Nahiyar Afrika ta Yamma watau WAEC, ya bayyana cewa su na shirin ganin yadda za su koma amfani da na’urorin zamani.

Dr. Iyi Uwadiae, yayi wannan jawabi a Ranar Litinin, 6 ga Watan Agusta, 2019, a lokacin da kungiyar AEAA da ke duba sha’anin ilmi a Afrika ta shirya wani taron shekara-shekara a Abuja.

A jawabin na sa, shugaban hukumar WAEC din ya fadakar da jama’a cewa kadan daga cikin dakunan jarrabawansu ne ke dankare da na’urorin zamani na ICT don haka ya ce su ke tanadi.

Iyi Uwadiae ya ke cewa dole sai an tabbatar duk makarantu da dakumam jarrabawa sun samu isassun kayan aiki kafin a yi hijira zuwa tsarin gudanar da jarrabawa ta hanyar amfani da gafaka.

KU KARANTA: An nada sababbin shugabannin manyan makarantun jihar Zamfara

"Idan a ka sauya zuwa tsarin zamani ba tare da Dalibai ko makarantu sun yi isasshen tanadi ba, a na iya samun tasgaro. Yanzu haka WAEC ta na shirya jarrabawa ne a kasashen Afrika har biyar.:

“Mu na kokarin wayar da kan ‘ya ‘yan sauran kasashen na mu inda mu ke kokarin ganin sun bi sahun sauran jama’an ta yadda ‘dalibai da makarantu za su samu kyakkyawan shiri” Inji Uwadie.

Dr Uwadiae ya ke cewa jarrabawar da WAEC ta ke shiryawa duk shekara ya na zuwa ne da mataki daban-daban wanda su ka hada da tsarin dogon rubutu, da zabi-ka-tika da jarrabawar gwaji.

Yanzu dai hukumar JAMB ta na shirya jarrabawan shiga makarantun gaba da sakandare ne da na’urorin zamani. An fara wannan tsari ne a wasu tsirarrun wurare kafin tsarin ya gama ko ina.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel