Masana: Za a fito da maganin kansa, da na hana mutuwa da tsufa

Masana: Za a fito da maganin kansa, da na hana mutuwa da tsufa

Wasu rikakkun Masana 2 da a ke ji da su yau a Duniya; José Cordeiro da kuma David Wood sun bayyana cewa nan da shekaru 27 Bayin Allah za su daina mutuwa idan har sun ga dama.

Wadannan kwararru sun bayyana wannan ne a wajen kaddamar da wani littafi da su ka gabatar mai suna ‘The Death of Death’, ma’ana ‘Mutuwar mutuwa.’ An yi wannan taro ne a Kasar Sifen.

Kamar yadda Masanan su ka bayyana, nan da shekarar 2045, mutum zai iya zaban ya ki mutuwa ko kuma ya maida kansa yaro bayan ya tsufa. José Cordeiro Malamin jami’ar MIT ne a Amurka.

Wadannan kwararru biyu da su ka kirkiro manhajar ‘Symbian’ a Duniya sun nuna cewa babu shakka kimiyya ya tabbatar za a iya daina mutuwa. Kuma za a cin ma hakan ne ba da dadewa ba.

KU KARANTA: An kama wani Malami Mai kwanciya da Almajirai a Makaranta

Masanan sun ce za a rika dauke kwayoyin garkuwan rayuwa wadanda ba su da kyau daga jikin ‘Dan Adam, za dasa wasu dabam masu lafiya, wanda a haka ne za a yi maganin mutuwa a Duniya.

A wajen kaddamar da wannan littafi, Cordeiro da Woods sun bayyana cewa idan a ka cin ma wannan mataki, babu yadda za a yi mutum ya mutu haka kurum idan ba ya gamu da hadari ba,

Haka zalika wadannan zakakuran Masana sun ce an gano yadda za ayi maganin tsufa ta hanyar yi wa kwayoyin halitta siddabaru. An dai dade a na tunanin yadda za a kai ga wannan mataki.

Ba a nan kadai ilmin wadannan kwararru a fasaha ya tsaya ba, inda su ka ce nan da shekaru goma, za a gano maganar kansa. Sai dai magungunan mutuwan da cutar za su yi tsada a farkon fitowarsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel