Hajjin Bana: Sojojin Najeriya 348 sun isa kasar Saudiyya don sauke farali

Hajjin Bana: Sojojin Najeriya 348 sun isa kasar Saudiyya don sauke farali

Tawagar Rundunar Sojojin Najeriya wadanda suka samu ikon zuwa aikin hajjin bana sun isa birnin Madinah na kasar Saudiyya.

Sojojin guda 348 sun sauka ne a filin tashi da saukan jirage na Yarima Mohammed Abdulaziz a safiyar ranar Alhamis.

Sun baro Legas ne a ranar Laraba cikin jirgin Flynas mai lamba XY5133 da ke dauke da maniyyan jihar Ogun guda 150.

Sojojin sun isa kasa mai tsarkin a lokacin da ake fama da matukar zafin rana a kasa mai tsarki wadda ta tilastawa maniyattan yawan fita waje kafin rannaku shida na karshe na aikin hajjin.

DUBA WANNAN: Zaben Kano: Kotu ta aike wa INEC da Kwamishinan 'Yan sanda sammaci

Tawagar maniyyatan na sojojin Najeriya ta kunshi maza 189 da mata 159.

Hukumar Kula da Jin Dadin Maniyatta ta Najeriya (NAHCON) ta ce a halin yanzu maniyyatan Najeriya 33,000 ne suka isa kasa mai tsarki domin sauke faralin.

Sojojin sun sauka ne a rukunin gidaje na Elyas Residential and Commercial Centre.

Kasashen Indiya, Bangladesh, Tunusia, Iran da Pakistan duk suma sun sauke maniyyatan su ne a rukunin gidajen na Elyas.

A halin yanzu, Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya ta shawarci maniyatta su rika shan ababen sha da rage shi rana ta hanyar amfani da lema saboda zafin rana da ake fama da shi.

Misali zafin yanayi a birnin Madina a ranar Alhamis ya kai ma'aunin celsius 44°C yayin da a Madina kuma ya kai 41°C.

Hasashin yanayi a biranen biyu ya nuna cewa za a rika samun yanayin zafi na 43°C a cikin kwanaki 10 nan gaba kafin karshen watan Dhu al-Hijjah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel