Dangote zai ware 53% na danyan mai a matatarsa wajen hada fetur

Dangote zai ware 53% na danyan mai a matatarsa wajen hada fetur

Mun samu labari cewa Kamfanin Dangote ya bayyana cewa zai fitar da kashi 53% na danyan man da zai rika tacewa a matatarsa wajen samar da man fetur da zarar an fara aiki a matatar da a ke yi a Legas.

Kamfanin ya yi wannan magana ne ta bakin babban shugaba watau Aliko Dangote. Alhaji Dangote ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya kai ziyara zuwa Hedikwatar ofishin kamfanin man Najeriya.

Aliko Dangote ya kuma bayyana cewa ba takara ya ke yi da kamfanin NNPC na Najeriya wajen tace mai ba. Idan an kammala aikin matatar Dangote, duk rana za a rika tace danyen mai ganga 650, 000.

53% na man da za a tace zai samar da man fetur a Najeriya, hakan na nufin a duk rana ta Allah, za a samu ganga 344, 500 na man fetur. Wannan adadin ya fi duka abin da kasar ta ke iya tacewa a rana.

Matatan gwamnatin Najeriya da ke hannun kamfanin NNPC su na iya tace gangunan mai 445,000 kadai a kullum. Da zarar an gama aikin Dangote, matatar ta Legas kurum za ta tace fiye da ganga 600,000.

KU KARANTA: Aliko Dangote ya yi wa ‘Yan kwallon Super Eagles ruwan kudi

“Muhimmin abu a wajen mu shi ne mu hada kai mu yi aiki da NNPC; ba wai mu yi kokarin ganin yadda za mu yi takara da kamfanin NNPC ba. Za mu so ne mu yi aiki tare da juna a zama tamkar guda.”

Dangote ya rufe jawabin sa da cewa: “A haka ne kurum kowa zai samu nasara.” Najeriya ta na da kamfanonin da ke tace danyen mai ne a Garin Warri da Kaduna da kuma wasu 2 a Garin Fatakwal.

Shi ma shugaban kamfanin NNPC na yanzu, Mele Kolo Kyari, ya bayyana cewa gwamnati ba ta harin hannun jarin kamfanin tace man da Dangote da ya ke ginawa. Kyari ya ce za su yi aiki ne tare da juna.

“Aikin da ke gaban NNPC shi ne ta hada karfi da karfe da irin su Dangote wajen ganin Najeriya ta shiga cikin sahun kasashen da ke fita da man fetur zuwa kasashen ketare.” Inji Malam Kolo Kyari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel