Ina taya ka murna ‘Danuwa na - Mufti Menk ya fadawa Isa Pantami

Ina taya ka murna ‘Danuwa na - Mufti Menk ya fadawa Isa Pantami

Fitaccen Malamin nan na Musulunci na Duniya, Mufti Menk, ya tofa albarkacin bakinsa bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin Minista.

Shehin Malamin Mufti Menk ya fito shafinsa na Tuwita ya na taya shugaban NITDA, Isa Ali Pantami murna gaban Duniya. Ga abin da Malamin na kasar Zimbabwe watau Mufti Menk ya ke cewa:

Ina taya ‘Danuwa na Dr Isa Ali Pantami (@DrIsaPantami) murna a kan tantance shi da a ka yi a matsayin Ministan gwamnatin tarayyar Najeriya. Fiye da mutane dubu biyu su ka nanata wannan sako.

Malamin bai tsaya a nan ba kawai, inda ya cigaba da cewa: Ubangiji Allah ya dafa maka wajen ganin yin aikin da ya dace a kowane lokaci. Malamin ya karasa addu’ar ta sa da cewa “Ameen! #Tabarakallah #Nigeria #Pantami”

KU KARANTA: Wani Malamin addini bai goyi bayan haramta kungiyar Shi’a ba

Dr. Isa Pantami babban Malami ne na addinin Musulunci wanda ya tara ilmin Al-kur’ani bayan ya yi zurfi a ilmin Boko. Pantami ya yi karatu ne a jami’o’in kasar waje, daga ciki har da irinsu kasar Ingila.

Fiye da mutum dubu tara su ka nuna sha’awarsu kan wannan sako da Mufti Menk ya aikowa takwaran na sa wanda majalisa ta tantancesa a matsayin Minista a Ranar Juma’a 26 ga Watan Yuli, 2019.

Shi ma Isa Ali Pantami a shafin sa na Tuwita watau @DrIsaPantami, ya ji dadin wannan addu’a da Shehin ya yi masa inda ya yi godiya, ya kuma nemi Malamin ya cigaba da shi a cikin addu’o’insa a kullum.

@DrIsaPantami ya rubutawa @muftimenk amsa da cewa: “Ameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum, ‘Danuwana. Don Allah ka da ka manta da mu a cikin addu’o’inka. Allah ya cigaba da datar da kai a kan tafarkin daidai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel