Alkawarin Umrah: An yi wa ‘Dalibar da ta yi suna kan Abba Gida-gida takardun fita Najeriya

Alkawarin Umrah: An yi wa ‘Dalibar da ta yi suna kan Abba Gida-gida takardun fita Najeriya

Kaunar ‘dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Kano da a ka yi watau Injiniya Abba Kabir Yusuf, ta sa wata Baiwar Allah ta yi suna kuma har za ta keta hazo domin sauke farali.

Idan ba ku manta ba kwanakin baya wata ‘yar makaranta mai suna Rafiatu Bello Danjuma ta rika yawo a gari bayan da a ka ga Hijabin ta dauke da sunan Abba Gida-Gida lokacin da ta kammala Sakandare.

A dalilin haka ne wani Bawan Allah ya dauki nauyin kai ta kasa mai tsarki domin ta yi Umrah. Kawo yanzu mun samu labari cewa har an yi wa wannan Budurwa takardun fasfo na fita daga cikin Najeriya.

Usman Abdulganiyyu Yaro, shi ne wanda ya fito shafinsa na sada zumunta na Tuwita ya bayyana cewa an kammala takardun Rafiatu Bello mai shekaru 20 da haihuwa da ke zaune a cikin Birnin Kano.

KU KARANTA: Malamai sun koma rai hannun Allah saboda rashin albashi

Alkawarin Umrah: An yi wa ‘Dalibar da ta yi suna kan Abba Gida-gida takardun fita Najeriya
Rafiatu Bello 'yar shekaru 20 mai son Abba Gida-gida za ta tafi Umrah
Asali: Facebook

Malam Usman Abdulganiyyu Yaro ya kuma nuna cewa wani fitaccen ‘Dan siyasa mai suna Honarabul Miko Tarauni ne ya dauki nauyin fitar da wannan yarinya mai kaunar Abba Gida-Gida zuwa waje.

Abba Kabiru Yusuf shi ne ‘dan takarar da tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar PDP a Arewacin Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso ya marawa baya a zaben 2019, amma ya sha kasa a hannun APC.

Duk da haka wannan ‘dan takara ya samu tsananin karbuwa a cikin Kano musamman a wajen mabiya ‘darikar Kwankwasiyya irin su Miko Tarauni Mai Daraja har wannan Budurwa ta ci albarkacinsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel