Saudi Arabia za ta shirya Gasar Musabaqah da na kiran Sallah a 2019

Saudi Arabia za ta shirya Gasar Musabaqah da na kiran Sallah a 2019

Mun samu labari cewa Saudi Arabia za ta gudanar da wata katafariyar Gasar Musabaqah na karatun Al-Qur’ani mai girma da kuma Gasar musamman na kiran sallah domin Ladanai.

Gwamnatin kasar Saudiyya a karkashin babbar hukumar nan ta shakatawa wata GEA ce za ta shirya wannan babban Gasa wanda kasashe daga fadin Duniya za su gwabza a kasa mai tsarkin.

A wani jawabi da hukumar ta GEA ta kasar ta fitar, an shirya wannan Gasa ne domin nunawa Duniya irin al’adun sauran kasashen Musulmai. Jakadan Najeriya ya sanar mana da wannan.

Ambasada Adnan Bostaji mai wakiltar Najeriya a Saudi ya sanar da kasar nan game da wannan shiri da kasar Larabawan ke yi. Wannan duk ya na cikin sababbin manufofin gwamnatin kasar.

KU KARANTA: Musulmai sun yi kira ga Buhari ya yi koyi da wani Gwamnan Arewa

An ware kyautar kudi har fam Riyal miliyan 5 watau fam miliyan 1.3 na Dalar Amurka ga wanda ya yi nasara a Gasar Musabaqar. Wanda ya lashe Gasar Musabaqah zai samu akalla Dala 530, 000.

Kawo yanzu an samu kwararru a wannan bangarori har 21, 000 da su ka aiko takardun shiga Gasar daga kasashe 162. Za a yi wannan Gasa ne daga karshen Agustan bana zuwa Satumba.

Mutane 11, 000 da su ka aiko takardun na su, manyan Alaranmomi ne yayin da sauran mutane 9, 000 kuma su ka kware a kiran sallah watau Ladanci kamar yadda rahotan Daily Trust ya nuna.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel