Kungiyoyin NASU da SSANU za su shiga yajin aiki a Jami’ar ABU Zaria

Kungiyoyin NASU da SSANU za su shiga yajin aiki a Jami’ar ABU Zaria

Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’in gwamnatin Najeriya na SSANU da NASU na bangaren jami’ar Ahmadu Bello University da ke Garin Zariya sun sha alwashin shiga yajin aikin da za a zoma.

Shugabannin kungiyoyin SSANU da NASU na sashen ABU Zariya sun bayyana cewa da su za a burma cikin yajin aikin da za a fara a ko ina a fadin jami’o’in gwamnatin tarayyar da ke Najeriya.

Shuaibu Halilu wanda shi ne shugaban kungiyar SSANU na jami’ar, ya bayyanawa Manema labarai cewa sun dauki wannan mataki ne bayan manyan kungiyar sun yi wani taron musamman.

Malam Halilu ya fadawa Jaridar Daily Trust cewa gwamnatin tarayya ta nuna son-kai wajen warewa Ma’aikatan jami’o’i alawus din da a ka fitar kwanan nan. Halilu ya ce an fifita Malamai.

KU KARANTA: Uwargidar Shugaban kasa ta aikawa Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya wani sako

A cewarsa ba a yi adalci ba idan a ka bar Malaman makaranta su ka dauki 80% na alawus din da a ka ba jami’o’in gwamnati yayin da sauran kanana da manyan ma’aikata a ka bar su da 20% rak.

A madadin kungiyar ta SSANU, Halilu ya tabbatar da cewa babu abin da zai sa a gan su a bakin aiki da zarar an buga gangar yajin aiki a sauran jami’o’in da ke kasar da ke karkashin kungiyoyin.

A yanzu dai ‘yan majalisar wakilai tarayya da dattawa su na ta faman kira ga Ma’aikatan jami’o’in na SSANU da NASU da su janye shirin shiga yajin aikin da zai jagula karatun ‘Daliban kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel