Wani jigon APC yayi cakacaka da Obasanjo, yace Buhari na iya bakin kokarinsa

Wani jigon APC yayi cakacaka da Obasanjo, yace Buhari na iya bakin kokarinsa

- Wani babban jigon jam'iyyar APC a jihar Lagas, Prince Tajudeen Olusi, ya yi martani ga wasikar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan rashi tsaro a kasar

- Olusi yace gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na iya bakin kokarinta a kasar

- Yayi zargin cewa wasu masu adawa da gwamnati mai mulki ne ke dada rura wutar fitina a kasar

Wani babban jigon jihar Lagas, Prince Tajudeen Olusi, ya nuna rashin amincewa da ikirarin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan rashi tsaro a kasar.

Yace duk da cewar tsohon shugaban kasar ya kasance babban jigo a kasar kuma shugaba mai fadin ra’ayinsa, toh hukuncinsa akan rashin tsaro cikin wasikar da ya rubuta na cike da kura-kurai.

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, Olusi wanda ya kasance Shugaban kungiyar dattawan APC a Lagas ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari na iya bakin kokarinta domin magance rashin tsaro a kasar.

Yayi kira ga yan Najeriya da su tallafa wa gwamnatin tarayya a kokarinta ta hanyar fallasa wadanda ya zarga da rura wutar rashin tsaro saboda adawarsu da gwamnati mai mulki.

“Duk koke-koken da ake a hare-hare da rashin tsaro, wasu da ke adawa da gwamnati mai mulki ne suka shirya shi,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ya yi magana bayan Gwamnan PDP ya fadi abin da ya mallaka

Olusi ya nuna yakinin cewa duk da hasashen da ake tayi cewa Najeriya na iya rabuwa saboda yawan hare-hare da kashe-kashe, babu wani abun tashin hankali.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel