Gwamna Yahaya ya nada shugaban ma'aikata da wasu sabbin hadimai hudu

Gwamna Yahaya ya nada shugaban ma'aikata da wasu sabbin hadimai hudu

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Gombe, Alhaji Abubakar Inuwa Yahaya, ya amince da nadin Alhaji Abubakar Inuwa Kari a matsayin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Gombe.

Kafin nada shi a sabon mukamin, Kari ya kasance darektan tsare-tsare a sakatariyar jam'iyyar APC ta kasa.

Kari ya maye gurbin Alhaji Muhammad Kabir Usman Kukan Daka, mutumin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada domin ya wakilci jihar Gombe a hukumar tsara rabon kudaden gwamnatin tarayya da aka samu daga haraji (RMAFC).

A ranar 2 ga watan Yuni ne, gwamna Yahaya ya nada Kukan Daka da wasu mutane 12 a matsayin sahun farko na mukaman da ya nada bayan rantsar da shi a matsayin zababben gwamnan jihar Gombe.

DUBA WANNAN: Tura ta kai bango: Kungiyar dattijan arewa ta umarci makiyaya su bar kudancin Najeriya

A wani jawabi da Ismaila Uba Misilli, kakakin gwamna Yahaya, ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya amince da nadin wasu uku a matsayin mataimka na musamman, mutum guda daga sanatoriya uku na jihar.

Mutanen da gwamnan ya nada sune: Adamu Abdullahi Masad Biri (Gombe ta arewa), Babaiya Kombani (Gombe ta tsakiya), da Abdullahi Idris Maitama Billiri (Gombbe ta kudu).

Kazalika, gwamnan ya amince da nada Umar Chiroma Abdussalam a matsayin shugaban sashen sufuri na jihar Gombe (Gombe line)

A cewar sanarwar, dukkan sabbin nadin zasu fara aiki nan take, ba tare da bata lokaci ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Za ka iya aiko mana da labari ta hanyar cike wanna fom da ke kasa:

https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSch6m8qBDJY3fmT8OH0Dy7Sqkrvwt-tveaPURetOsKjYb_4cQ/viewform

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel