Ana bikin murnar cika shekaru 50 da tura mutane duniyar wata a kasar Amurka
Ranar Talata 16 ga watan Yulin 2019 aka cika shekaru 50 cur da Amurka ta tura wasu mutanen ta uku zuwa duniyar wata bayan da ta harba su a cikin wani Kumbo.
Kasar Amurka ta harba Kumbon da aka yiwa lakabi da Apollo 11 dauke da mutane uku zuwa duniyar wata daga babbar tashar sararin samaniya ta Kennedy Space Center dake jihar Florida a ranar 16 ga watan Yulin shekarar 1969.
A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da shagulgulan tunawa da wannan babbar rana a kasar Amurka.
Jaridar RFI Hausa ta ruwaito cewa, Buzz Aldirin mai shekaru 89 da Michael Collins mai shekaru 88, sun sake haduwa a ranar Talata a dai dai wurin da aka harba su zuwa duniyar wata shekaru hamsin da suka gabata.
Sai dai jagoran wannan matafiya, Neil Amstrong, ya riga mu gidan gaskiya tun a shekarar 2012 wanda ya kasance mutum na farko da ya fara sanya sawayen sa a duniyar watan.
Kumbo Apollo 11 ya isa duiyar wata bayan shafe tsawon kwanaki hudu bayan barin cibiyar hukumar kula da tashar sararin samaniya ta NASA dake birnin Florida na kasar Amurka.
Har ila yau, babu kasar da ta kamanta wannan abun zo-a-gani bayan dawowar mutanen uku zuwa duniya a shekarar 1972.
KARANTA KUMA: Mai juna biyu ta kone kurmus, hatsarin mota ya raunata mutane 8 a Ibadan
Ana iya tuna cewa, a shekarar 1989 da kuma 2004, shugabannin kasar Amurka George H.W Bush da kuma dan sa, George Bush, sun gaza cika kudirin su na sake aikewa da wasu 'yan kasar zuwa duniyar wata yayin da hakar su ba ta cimma ruwa ba a sanadiyar rashin samun goyon baya daga majalisar tarayya ta kasar a lokutan da suke mulki.
Za a shafe tsawon mako guda ana gudanar da bikin tunawa da wannan rana a kasar Amurka.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng