Zainab Hamisu: Matashiyar da ta cika jim kadan bayan ta yi aure

Zainab Hamisu: Matashiyar da ta cika jim kadan bayan ta yi aure

Kwanaki kusan 105 da yin auren Zainab Hamisu Malumfashi da masoyinta mai suna Nuhu Garba Sani, sai Ubangiji ya karbi rayuwarta yayin da ake tsakiyar watan Ramadan.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Zainab Hamisu Malumfashi ta cika ne a ranar 15 ga watan Mayun 2020, a wani asibiti. Wannan rana ta zo daidai da ta 23 ga watan Ramadan, 1441.

Mai dakin marigayiyar, TPL Garba Sani ya bayyana cewa bayan sun yi sahur da sallar dare a ranar Juma’a, sai ta karanta Al-Qur’ani, daga nan ne su ka yi sallar Asuba da gari ya waye.

Bayan sallar asuba kwatsam sai Zainab Hamisu ta ce ga garinku nan. Ana tunanin cewa matsalar juna biyu ce ta bijirowa wannan mata har ya kai ga ta rasa rayuwarta a safiyar Juma’ar.

Garba Sani ya fito shafinsa na sadarwa na Tuwita ya na yabon halin mai dakinsa, wanda da-dama su ka shaida cewa lallai mutumiyar kirki ce, mai tausayi, ta kuma san darajar mutane.

KU KARANTA: Wata ta shayar da Marayu 20 mama bayan an kashe Iyayensu

Iyayen Zainab Hamisu su na zama ne a garin Funtuwa, arewacin jihar Katsina. A ranar 1 ga watan Fubrairun 2020, ta auri sahibinta wanda ta ke gidansa na sunnah a lokacin da ta cika.

Rahotanni sun bayyana mana cewa marigayiyar ta yi karatun digirinta a fannin ilmin kananan halittu ne a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ta kuma kammala makarantar a 2018.

Kamar yadda mutane su ka san ta da Zee ko kuma Zeehams, marigayiyar ta na da kamfanin kwalliya inda ta ke yi wa ‘yan mata ado. Marigayiyar ta shahara da wannan aiki na ta.

Wata wanda ta ke bibiyar kamfanin kwalliyar marigayiyar ta bayyana cewa ta kasance mace mai riko da addini domin a dalilin haka ne ba ta yi wa mata kwaskwarima a gashin girarsu.

Bayin Allah sun yi wa Nuhu Garba Sani ta’aziyyar wannan rashi da ya yi, inda kuma ake cigaba da yi wa mata addu’ar samun rahama a wannan wata mai daraja wajen duk musulmai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel