Christine Lagarde ta yi murabus daga Hukumar lamunin Duniya IMF

Christine Lagarde ta yi murabus daga Hukumar lamunin Duniya IMF

Labari ya zo mana daga babban birnin Washington na kasar Amurka cewa Christine Lagarde ta sauka daga kan kujerarta na shugabar hukumar lamuni ta Duniya wanda a ka fi sani da IMF.

Christine Lagarde mai shekary 63 ta yi murabus da hukumar IMF ne domin ta zama shugabar babban bankin Nahiyar Turai. A na sa rai cewa Lagarde ce za a ba shugabancin wannan banki.

Yanzu haka tuni Lagarde ta fara ragewa kan ta aiki a IMF kuma har ta kai ta bayyana babban mataimakinta watau David Lipton a matsayin Mukaddashin babban Manaja na hukumar ta IMF.

A wani jawabi da Lagarde ta karanto ranar Talata, 16 ga Watan Yuli, 2019, ta bayyana cewa ta ajiye aikin ne domin masalahar kan-ta da kuma wannan hukuma inda ta ke sa rai a fito da Magajinta.

KU KARANTA: Za a kira wani babban taron sha'anin tsaro a Najeriya

Misis Lagarde za ta bar wannan matsayi na ta ne a Ranar 12 ga Watan Satumban bana. Lagarde ta dade a kan wanna kujera tun 2011 lokacin da ta karbi aiki daga hannun Dominique Strauss-Kahn.

A lokacin da ta ke kan wannan mukami ne hukumar lamunin ta hada kai da kungiyar kasashen Turai da kuma babban bankin Nahiyar ta Turai watau ECB wajen ceto tattalin arzikin kasar Girka.

IMF ta taimakawa kasar da bashin kudi ne a lokacin da ta shiga cikin wani hali na matsin lambar tattalin arziki. Lagarde Lauya ce kuma ‘Yar siyasa sannan Masaniya a kan harkar tattalin arziki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel