Ku bar zarginmu da kashe-kashe – Shugaban Fulani

Ku bar zarginmu da kashe-kashe – Shugaban Fulani

-Sarkin Fulanin Legas ya yiwa Reuben Fasoranti ta'aziyya kan mutuwar diyarsa wadda 'yan bindiga suka hallaka

-Kungiyar Afenifere tayi magana a kan cewa fulani makiyaya na da sa hannu a kan kisan inda ta gargadi Tinubu da ya bar kokarin kare makiyayan daga ire-iren laifukan da suke aikatawa bayan yayi wata magana mai nuna yana goyon bayan fulanin

Alhaji Muhammad Bambado, Sarkin Fulanin Legas kuma Shugaban Fulanin yankin Kudu maso yammacin Najeriya ya yi kira ga jama’a da su daina daura wa Fulani laifin kashe-kashen da ake a kasar nan.

Wannan kiran yazo ne a daidai lokacin da kungiyar Yarbawan nan ta Afenifere ta yi martani ga jagoran APC wato Bola Tinubu yayin da yake cewa bai kamata ana batawa fulanin kasar nan suna ba.

KU KARANTA:Na san ‘yan siyasan da suka zama biloniyoyi a dare daya – Amaechi

Tinubu a lokacin da yake jaje ga Fa Reuben Fasoranti a kan mutuwar diyar shi, Misis Funke Olakunri, yace kuskure ne a koda yaushe a rika danganta laifukan garkuwa da mutane da kuma kashe-kashe zuwa ga Fulani makiyaya.

Haka zalika, wannan batu na Tinubu bai wa kungiyar Afenifere dadi ba ko kadan, inda ta yi gargadi ga tsohon gwamnan jihar Legas din cewa kada ya rika boye ta’adin da Fulani suka kawo a yankin Kudu maso yamma.

Kungiyar wadda ta fitar da wani zance mai tsawo ta hanyar Sakataren labaranta, Yinka Odumakin cewa yayi, “ Maganar kada a fadi laifin Fulani makiyaya ba ta ma taso ba kuma ana maganar kisan diyar shugabanmu ne ba maganar siyasa ake ba.”

Har ila yau, shi kuwa Sarkin Fulanin Legas, a na shi jawabin cewa yayi mutane su bar daura wa Fulani laifin da ba su aikata ba.

A kalamansa na ta’aziyya kuwa ga mahaifin marigayiyar cewa yayi: “ A madadin ni kaina da ilahirin al’ummar fulain dake Kudu maso yamma muna taya ka juyayin wannan rashi da fatan kuma Allah ya sa ta huta, amin.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel