Tun 2015 mu ka fara wannan shiri inji wadanda su ka kera motar lantarki

Tun 2015 mu ka fara wannan shiri inji wadanda su ka kera motar lantarki

Shugaban bangaren kere-kere na MRG a tsangayar kanikanci ta jami’ar UNN da ke Nsukka a Najeriya, Injiniya Ozoemena Ani, ya bada labarin yadda su ke kera mota mai aiki da lantarki.

Injiniya Ozoemena wanda ya ke daf da zama Farfesa a jami’ar Nsukka ya yi bayanin yadda su ka kirkiro mota mai amfani da wutar lantarki a maimakon fetur. An sa wa wannan mota suna LION.

Ozoemena Ani ya bayyana cewa tun a 2015 shugaban jami’ar UNN ya nemi Malaman makarantar su rika yin binciken da zai taimakawa al’umma don haka su ka kafa gungu su ka soma tanadi.

Malamin ya fadawa Daily Trust cewa tsohon VC na jami’ar UNN, Farfesa Benjamin Chukwuma Ozumba, shi ya tunzura su, su ka kai ga wannan aiki wanda yanzu ya kai ga zama zahiri.

Shehin Malamin ya ce sun sayo kusan 80% na kayan kera wannan mota ne a kasuwannin Onitsha, Nnewi da Nsukka, yayin da su ka nemo wasu daga kasar Sin, a ka yi masu kwaskwarima.

KU KARANTA: A na kokarin rage barkowar makamai a cikin Najeriya

Injiniyan ya nuna cewa sun sha wahala wajen mola ainihin karafunan da za su yi wa wannan mota daidai, don haka ya nemi hadin gwiwa da hukumar NADDC da kuma kamfanin INNOSON.

Shugaban hukumar NADDC masu kere-keren motoci a Najeriya, Aliyu Jelani, ya yabawa wannan kokari da Malaman jami’ar UNN su ka yi, ya na mai kira ga sauran makarantu su yi koyi da su.

Haka zalika shugaban jami’ar ta Nsukka na yanzu, Farfesa Charles Igwe, ya yi farin ciki da aikin da Mutanensa su ka yi. Igwe ya yi alkawarin kara ba Injiniyoyin kwarin gwiwar wannan fasaha.

Wannan Malami ya ke cewa nan gaba kadan za su gyara surar motar, sannan kuma su nemi a fara saida ta a kasuwa. Yanzu dai wannan mota “Lion Ozumba 551” ta hau hanya kuma ta na aiki sarai.

Lion Ozumba 551 ce motar farko a kasar da a ke tuka ta da karfin wutar lantarki a madadin mai. A wasu kasashen dai an yi nisa a irin wannan fasaha inda tuni a ka san da irin wannan motoci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel