Wata sabuwa: An shiga takun saka tsakanin Abdulmuminu Kofa da gwamna Ganduje

Wata sabuwa: An shiga takun saka tsakanin Abdulmuminu Kofa da gwamna Ganduje

Sabon rikici ya kunno kai a cikin jam'iyyar APC a Kano tsakanin dan majalisar wakilai na mazabar Kiru/Bebeji, Abdulmumini Jibrin Kofa, da gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a kan kujerar shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai.

Rikicin jam'iyyar ya kara fitowa fili bayan Kofa ya yi yunkurin canja shugabannin jam'iyyar APC a mazabarsa ta Kiru da Bebeji.

Dan majalisar da Ganduje sun samu rashin jituwa ne a kan batun zabin wanda zai zama shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai tsakanin dan majalisar wakilai daga mazabar Fagge, Honarabul Aminu Goro, da Honarabul Alhassan Ado Doguwa, dan majalisar wakilai na mazabar Doguwa/Tudunwada.

Gwamna Ganduje ya goyi bayan Doguwa tare da jingine Goro, dan majalisar da Kofa ya so ya zama shugaban marasar rinjaye a majalisar wakilai.

Zaman Doguwa shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai bai yi wa Kofa dadi ba, musamman ganin muhimmiyar rawar da ya taka wajen samun nasarar Femi Gbajabiamila, shugaban majalisar wakilai.

A wani yanayi mai kama da daukan fansa, Kofa ya gaggauta cire shugabannin jam'iyyar APC masu biyayya ga gwamna Ganduje a mazabar Kiru/Bebeji tare da kafa wasu sabbi masu biyayya gare shi.

DUBA WANNAN: Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta

Sai dai, shugabannin da Kofa ya canja sun botsare masa tare da garzaya wa ofishin shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, tare da kai kukansu a ranar Talata.

Da ya ke gabatar da jawabi yayin da ya karbi bakuncin shugabannin da Kofa ya tsige, Abbas ya shaida musu cewa babu wanda ta isa ya cire su daga mukamansu.

Ana ganin cire shugabannin jam'iyya na karamar hukumar Bebeji da mazabar Kofa da honarabul Kofa ya yi zai kawo babbar baraka a jam'iyyar APC a jihar Kano.

Kokarin jin ta bakin dan majalisar a kan faruwar wannan lamari ya ci tura, saboda wayoyinsa basu shiga ba yayin da aka kira shi.

Kazalika, shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano ya ki cewa komai a kan batun, da aka tuntube shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel