Da gan-gan Gwamnatin APC ta kashe bangaren ilmi a Najeriya – ASUU

Da gan-gan Gwamnatin APC ta kashe bangaren ilmi a Najeriya – ASUU

Kungiyar nan ta ASUU ta Malaman Jami’an Najeriya ta bayyana cewa ba don nufin Talaka ya tsira a ka tsara manufofin harkar ilmi na gwamnatin nan ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.

ASUU ta yi wannan jawabi ne a Ranar Lahadin da ta gabata, 7 ga Watan Yuli, 2019, inda ta ce da gan-gan gwamnatin APC ta ke kin sakin kudi a bangaren ilmi domin a cigaba da barin al'umma a duhu.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar ta ASUU na reshen jami’ar Ibadan, Farfesa Deji Omole, wanda ya ce gwamnati ba ta damu da ilmin jama'a ba domin ta yi watsi da harkar.

Farfesa Deji Omole ya koka da yadda a ke fama da karancin Ma’aikata a jami’a da kuma rashin albashi mai tsoka. Farfesa Omole ya bada misali da jami’ar sa ta Ibadan da ke cikin wani hali a yanzu.

KU KARANTA: Wani Malamin addini ya ce dole Shugaba Buhari ya yi murabus

Shugaban na ASUU ya ce: “Manufar Gwamnatin APC na kin warewa harkar ilmi kudi, shiri ne na kashe jami’o’in gwamnati. Babbar Jami’ar Ibadan ta shiga cikin wani hali a yanzu saboda karancin kudi.”

“Ya zama ba a iya maye gurbin Malaman da su ka yi ritaya saboda gwamnati ta ki ware kudi domin cigaban jami’o’i da gan-gan.” Inji Deji Omole.

A cewar Omole, fiye da Yara 500, 000 su ke rasa damar shiga jami’ar gwamnati duk shekara a Najeriya, a na samun hakan ne saboda tabarbarewar wurin karatu da rashin isassun Ma’aikata a makarantun.

Farfesan ya gargadi gwamnati da cewa wannan hanya da ta bi zai kawo rashin aikin yi da barna a cikin kasa. Haka zalika Farfesan ya ce a sanadiyyar lodin aiki, Abokan aikinsu da-dama su ka mutu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel