Maniyyata 600 a cikin 1500 su ka biya kudin kujerun aikin Hajji a Taraba

Maniyyata 600 a cikin 1500 su ka biya kudin kujerun aikin Hajji a Taraba

Yayin da a ke shiryawa aikin hajjin wannan shekarar, mun samu labari cewa akwai jihohin da kawo yanzu ba su iya saida ko da rabin kujerun da a ka warewa Maniyyatan su a shekarar nan ba.

A jihar Taraba, akwai kujeru kusan 1000 da babu wanda ya iya saye a yanzu. Babban Sakataren hukumar da ke kula da aikin Hajji da walwalar Alhazai ta jihar, Umar Adamu Leme ya fadi haka.

A cewar Umar Adamu Leme, hukumar aikin Hajji na kasa watau NAHCON, ta warewa jihar Taraba kujeru 1, 575 ne a shekarar nan. Yanzu dai mutane 600 ne kadai su ka iya biyan kudin kujeru.

KU KARANTA: Masu shirin sauke farali sun fara barin Najeriya zuwa Saudi

Adamu Leme ya bayyana cewa har gobe a na cigaba da karbar Maniyyatan gwamnati da kuma masu bin jirgin yawo na ‘yan kasuwa. Za a soma jigilar Maniyyatan ne a karshen wannan Watan.

A na sa rai jirage su fara daukar wadanda za su tafi aikin Hajji ta jihar Taraba daga Ranar 23 ga Watan Yuli, 2019. Hukumar Alhazan ta na kira ga jama’a su yi maza su kammala biyan kudin su.

A jihar Taraban dai ku na da labari cewa mahajjatan za su biya kudi N1,523, 598, 10 a wannan shekarar. An cin ma wannan farashin kujera ne bayan hukumar NAHCON ta rage kudin hajjin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng