Babbar magana: Daga yin wasa da lamarin aure Zainab da Sunusi sun angwance a shafin Facebook

Babbar magana: Daga yin wasa da lamarin aure Zainab da Sunusi sun angwance a shafin Facebook

- Daga yin wasa da lamarin aure a shafin Facebook, Zainab da Sunusi sun angwance babu shiri

- Matasan sun nuna cewa zasu yi aure a shafin Facebook inda kowa ya kawo waliyyinsa aka daura aure, shaidu suka shaida

- Daga baya matasan sun nuna cewa wasa suke, sai dai Malamai sun bayyana cewa aure ya dauru babu shakka

Yadda lamarin ya kasance shine, jiya da yamma Gen. Sunusi da Zainabu Abu suka bada sanarwar za a daura musu aure kowa yazo da waliyyinsa.

Haka kuwa aka yi saurayin ya kawo wakilinsa mai suna Ismail Auwal Sarki, sai ya nema masa auren Zainab a wajen waliyyinta mai suna Mukhtar Y Buharista kamar dai yadda sigar neman aure ta kayyade.

Nan take waliyyin Zainab ya amince da bayar da auren, inda ya bawa Gen Sunus auren Zainab, kuma shaidu suka shaida a sashen comment.

KU KARANTA: Tirkashi murna za ta koma ciki: Kotu ta aikawa gwamnan Zamfara sammaci kan kujerar shi

Sai dai kuma daga baya saurayi da budurwar sun shiga wani hali, inda suke ta faman yin rubuce-rubuce a shafin na Facebook suna cewa ba auren gaske bane na wasa ne.

Amma kuma Malamai sun sanya baki akan lamarin, inda suka bayyana cewa auren Zainab da Sunusi ya dauru, saboda akwai Hadisin Manzon Allah (S.A.W) da yake cewa ba a wasa da abubuwa guda biyu, daurin aure da kuma sakin aure.

To yadda lamarin ya kasance kenan, Allah kuma ya kyauta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng