Nayi karyar an sace ni ne saboda na samu kudin da zan bawa mijina yayi sana'a - In ji wata mata
- Wata mata da ta hada karyar cewa anyi garkuwa da ita ta shiga hannu
- Ta bayyana cewa ta yi karyar an sace ta ne saboda ta samu ta hada kudin da zata bai wa mijinta yayi sana'a
- Ta ce ta buga kowanne bangare ba ta samu aikin yi ba, duk da tana da kwalin digiri a bangaren lissafi
Wata mata mai suna Yemi Samuel, jami'an 'yan sandan jihar Kwara sun kama ta da laifin yin karya akan masu garkuwa da mutane sun sace ta.
Yemi wacce aka kai ta babbar helkwata ta hukumar 'yan sanda ta Akure babban birnin jihar Ondo, ta bayyana cewa ta hada cewa anyi garkuwa da ita ne, saboda tana so ta samu kudi daga gurin 'yan uwanta wanda za ta dinga taimakawa mijinta da ya bar aiki a jihar Kogi. Yemi ta ce mijinta bai samu kudin fansho da gwamnatin jihar take bayarwa ba na tsawon shekaru, hakan yasa suke zaune cikin kuncin rayuwa.
Yemi ta cigaba da bayanin cewa, 'yan uwanta wadanda suke da arziki, sun ki taimaka musu, hakan shine yasa ta yi kokarin cewa an sace ta. Inda ta gudu daga garinsu dake jihar Kogi ta je garin Ilorin babban birnin jihar Kwara domin ta boye a can, tunda babu wanda ya santa a can. Ta kama daki daya haya, inda ta ke amfani dashi tana kiran 'yan uwanta.
KU KARANTA: Zamfara: Ban bar bashin ko kwabo ba a Zamfara - Tsohon gwamna Abdulaziz Yari
"Nayi hakan ne domin na samu kudin da zai ba wa mijina ya fara sana'a. Na san 'yan uwanmu suna da arziki, kuma idan har na ce musu an sace ni dole za su hada wannan kudi domin a sako ni.
"Naira miliyan daya kawai na bukata a gurinsu, amma kuma an zo an kama ni. Na san nayi laifi, amma ina ganin wannan ita ce hanya daya da zan iya samo mana kudin, tunda aikin yi ya gagara," in ji ta.
Sai dai kuma kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa Yemi ta hada karyar an sace ta, amma an kamata a Kulende, dake yankin Sango cikin jihar Ilorin bayan ta bukaci naira miliyan biyar kudin fansa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng