Gwamnan Yobe zai kai mutane karatu zuwa Turkiyya da kasar Sin
Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya bada umarni a zabi mutum 700 ‘yan asalin jihar Yobe da za a ba gudumuwar yin karatu a kasashen waje. Daily Nigerian ta rahoto wannan labari.
Mai Girma Mala Buni zai aika asalin 'yan jihar zuwa kasashen Turai da Nahiyar Asiya domin su yi karatun Digiri da kuma Digir-gir da Digir-digir. Yanzu har an fara wannan shiri a jihar ta Yobe.
Sakataren hukumar da ke kula da gudumuwar karatun ‘Dalibai ta jihar Yobe, Alhaji Musa Mustapha, ya bayyana cewa gwamnati ta fara saida fam ga masu sha’awar fita waje su yi karatu.
Musa Mustapha ya ke cewa za a zabi mutane 500 ne da za su yi Digirin farko, yayin da za a zakulo wasu mutane 100 da za su yi Digir-gir na M. Sc, sai kuma jerin wasu 100 da za su samu PhD.
KU KARANTA:
Za a aika wadanda su ka samu wannan dama ne zuwa Makarantun da ke kasar Turkiyya, da China da kuma Tajikistan. Daga cikin sharudan da za a bi, dole ‘dalibi ya tanadi nasara a WAEC.
Mustapha ya kuma bayyana cewa a na bukatar ‘dalibai ne daga bangaren kiwon lafiya, kanikanci watau injiniya, ilmin komfuta, ilmin harkar noma da gona da kuma sauran bangarori na ilmi.
Wannan ya na cikin tsare-tsaren da gwamnatin jihar Yobe ta kawo bayan an rantsar da gwamna Mai Mala Buni, domin inganta harkar ilmi wanda ya kama hanyar shiga halin la-haula a jihar.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng