Ba a yi zabe a wasu yankunan Kaduna ba – Shaidu sun fadawa Kotu

Ba a yi zabe a wasu yankunan Kaduna ba – Shaidu sun fadawa Kotu

Yayin da a ke cigaba da shari’a game da zaben 2019 da aka yi. Jam’iyyar PDP mai adawa, ta gabatar da wasu daga cikin shaidunta a gaban kotun da ke sauraron korafin zaben jihar Kaduna.

Wani daga cikin wanda ya bada shaida a gaban kotun sauraron karar zaben ya bayyana cewa an yi zaben gwamnan jihar Kaduna ne cikin hatsaniya ba tare da an bar jama’a sun kada kuri’un su ba.

Wasu da-dama daga cikin wadannan shaidu sun fadawa kotu cewa a cikin Unguwar Kwarbai na Zariya da ake da akwatuna 26, ba a gudanar da zabe a mafi yawan wadannan rumfunan zabe ba.

Yahaya Abubakar, wanda ya yi wa PDP aiki a matsayin Wakili a zaben ya fadawa kotu cewa sakamakon zaben da aka shirya dabam da abin da ke cikin takardar da ta fito daga hannun INEC.

Wani shaida mai suna Mohammed M. Amfani, ya tabbatarwa kotu cewa ba a yi zabe a rumfa mai lamba ta 32 ba, inda kuma ya ce takardun da INEC ta fitar ba su kunshe da hatimin jami’an hukumar.

Haka zalika, Sadam Shehu ya ce: “A matsayina na WakiliN PDP, ina tabbatar da cewa, a Ranar 9 ga Watan Maris, ba ayi zabe a akwati na (001) ba.

Danjuma Garba, ya bada na sa shaidar inda ya ce sakamkon zaben da aka gudanar dabam da abin da INEC ta fitar. An canza kuri’un, sam ba haka zaben ya kasance ba. Inji Garba.

KU KARANTA: Kano: Nasarar Abba Gida-Gida ta kai gaban Kotun koli

”Sam jami’an INEC ba su zo rumfar mu ba, kurum sai mu ka ga sakamakon zabe daga baya. Babu hatimin INEC, sannan kuma babu sa hannuna a takardun da aka fitar” Inji wani Mohammed A. Dogara wanda ya bada shaida.

Tukur Mustapha shi ma ya fadawa kotu cewa ba ayi zabe a akwati na 006 ba.Ya ce: "INEC ba su kawo wasu kayan zabe zuwa rumfar mu ba. Amma a haka aka fitar da sakamako ba tare da sa-hannuna ba."

Shi kuma AbdulRahman Lawal, ya ce an yi zabe salin-alin a akwati na 003 kuma ya sa hannu, amma daga baya kurum sai ya ji labarin wani sakamakon dabam ya fita.

Bello Ubaidullah, wanda ya yi aiki a matsayin mai tattara kuri’u a zaben na bana ya ce a Unguwar Kwarbai ba a kirga kuri’un Mazabu bu domin kuwa jami’an tsaro sun tarwatsa kowa a lokacin/

Yanzu dai Alkali Ibrahim Bako da sauran masu sauraron karar sun karbi shaidu har 16, kuma za su cigaba da zama Yau, 19 ga Watan Yuni. Lauyan PDP, Elisha Kurah ya nuna cewa su na da shaidu 685.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel