Adamu Mua’azu yayi barazanar sanar da duniya faduwar PDP a zaben 2015 tun kan Jonathan ya kira Buhari

Adamu Mua’azu yayi barazanar sanar da duniya faduwar PDP a zaben 2015 tun kan Jonathan ya kira Buhari

Karin bayanai sun billo kan lamarin da yasa tsohon Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan ya yarda da shank aye a zaben 2015.

A baya bayanai daban-daban sun dunga fitowa daga bakunan manyan jami’ai kan yadda tsohon Shugaban kasar ya amince da sakamakon zaben har ya kira abokin adawarsa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin taya shi murnar yin nasara.

Sai dai kuma a yanzu gaskiyar zancen ya bayyana, inda ashe tsohon Shugaban jam’iyyar PDP, Adamu Mu’azu ne yayi barazanar sanar da duniya cewa babu shakka jam’iyyarsa ta sha kaye kuma sun yi na’am da sakamakon zaben.

A yanzu daya daga cikin wadanda suka taka rawar gani a lamarin, tsohon ministan shari’a Bello Adoke ya bayar da sabon bayani kan lamarin.

A hira da yayi da jaridar Premium Times, tsohon Adoke ya bayyana cewa tun a safiyar 31 ga watan Maris din shekarar 2015, shugaban jam’iyyar PDP Adamu Mu’azu ya same shi a ofishin sa inda ya fada masa cewa ga dukkan alamu fa Buhari ya kada su a zaben shugaban kasa amma kuma yaji kowa ya yi shiru ne sannan kasa ta dau zafi.

“Adamu ya ce ga dukkan alamu shugaban Kasa Jonathan ba zai yarda ya amince da an kada shi ba. Saboda haka ya ce da zaran karfe 5 na yamma ta yi Jonathan bai ce komai ba zai fito ya sanar wa duniya cewa jam’iyyar ta rungumi kaddara, APC ce ta yi nasara a zaben.

“Da yake ina daga cikin wadanda suke makusantar shugaban kasa a wancan lokaci kuma daya daga cikin mambobin kwanmitin tsaro na san illar da wannan furucin Mu’azu zai iya yi wa kasar nan idan har aka bari yayi haka.

“Dama kuma ko a wancan lokaci wasu na yi wa Adamu Mu’azu ganin yana yi wa jam’iyyar PDP zagon kasa. Kuma alokacin kasa ta dau zafi kan kowani bangare a kasar nan ya cika fam jira yake kawai komene ne ma ya faru.

“Bayan haka sai na garzaya kai tsaye zuwa ofishin Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki. Anan nayi masa bayanin cewa babu fa yadda za a yi a iya juya zaben nan. PDP ta sha kasa amma kuma shugaban kasa bai ce komai ba. Ana haka ne sai ministan harkokin jiragen sama Osita Chidoka ya kwada min kira ta waya selola ya ce in yi maza maza in taho fadar shugaban Kasa ana nema na cikin gaggawa. Na gaya masa cewa ina tare da maiba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro ne, nan dai bayan dan kankanin lokaci ya sake kira na.

“Daga nan sai ban tsaya ko ina ba sai fadar shugaban kasa. Ina shiga sai na iske Chidoka , Ministan Kudi, Ngozi Okojo-Iweala da mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo. Sannan kuma a gefen su a kai gwamnan jihar Akwa-Ibom, Godswil Akpabio.

“A lokacin ni na san abinda basu sani ba sai na ce wa Akpabio ya roki shugaban kasa ya hakura ya kira Buhari kawai aikin gama ya gama, sai ya ce gaskiya a bari tukunna a bashi lokaci. Daga nan sai na waiwaya gefen Namadi Sambo shima nace ko zai yi wa shugaban kasa magana cewa ya hakura ya fadi zabe. Sai ya ce sam ba zai hakura ba, abari kawai Jega ya bayyana sakamakon zaben amma ba zai kira Buhari ba a lokacin.

KU KARANTA KUMA: Wasu masu fada aji a kasar nan sun bukaci Kotu ta tsige Buhari saboda ya bai wa INEC takardun karya

“Ana haka ne sai wani mai hadimin Jonathan mai suna Dudufa ya waiwayo ya ce wa Jonathan, Baba, kayi hakuri zamu fice daga gidan gwamnati ranar 29 ga watan Mayu.

“Daga nan sai muka bazama dukkan mu da wadanda suke cewa ya kira Buhari da wadanda suke cewa kada ya kira shi. muka je gaban Jonathan.

“Yana ganin haka sai kawai ya tashi ya dauki waya ya mika yace a kira Buhari."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel