Kotu ta yanke wa barayin shanu biyu hukuncin shekaru 7 a gidan yari

Kotu ta yanke wa barayin shanu biyu hukuncin shekaru 7 a gidan yari

A ranar Juma'a 31 ga watan Mayu ne wata alkaliyar kotun Majistare ta yankewa wasu manoma biyu hukuncin zaman shekaru bakwai a gidan yari saboda satar shanu.

A yayin yanke hukuncin, Majistrate Hauwa Yusuf ta yanke wa Abdullahi Abubakar da Musa Shehu hukuncin bayan sun amince da aikata laifuka da suka hada da hadin baki, raunata wani da satar shanu.

Yusuf ba ta bawa masu laifin zabin biyan tara ba inda ta ce hakan zai zama darasi ga wasu masu niyyar aikata laifin.

DUBA WANNAN: Diyar Atiku ta ce ba za ta taba mantawa da mulkin APC ba

Dan sanda mai shigar da kara, Saja Bello Mohammed ya shaidawa kotu cewa wani Adamu Yusuf mazaunin Kudu Gari a karamar hukumar Mokwa ne ya shigar da kara a watan Afrilun 2018.

Mohammed ya ce wandanda aka yanke wa hukuncin sun raunata yaronsa yayin da ya tafi kiwo a daji da shanu 27 da tumakai 33.

Ya ce sun yiwa yaron mumunan rauni yayin da suka kai masa hari da adduna da sanda.

Mohammed ya ce wadanda aka yanke wa hukuncin sun daure yaron a daji sannan su kayi awon gaba da dabobin.

Ya ce jami'an 'yan sanda sunyi nasarar gano shanu 15 da tumakai 16.

Laifin ya sabawa sashi na 97 da 247 na Penal Code da sashi na 8 na dokar garkuwa da mutane da satar shanu na Jihar Niger kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel