Tsohon gwamna daga arewa ya goyi bayan kiran neman Oshiomhole ya yi murabus

Tsohon gwamna daga arewa ya goyi bayan kiran neman Oshiomhole ya yi murabus

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Sokoto, Malam Yahaya Abdulkarim, ya goyi bayan mataimakin shugaban jam'iyyar APC, Sanata Lawal Shu'aibu, a kan kiran neman shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshimhole, ya yi murabus.

Da yake gana wa da manema labarai a Sokoto ranar Alhamis, Abdulkarim ya ce Oshimhole ya nuna cewar ba zai iya shugabancin jam'iyyar APC ba.

"Ina goyon baya 100% a kan kiran neman Oshiomhole ya yi murabus domin jam'iyyar APC ta samu shugabanci nagari da zai kawo mata cigaba.

"Ya kamata a ce Oshiomhole ya jagoranci jam'iyyar APC ta samu karin gwamnonin jihohi, sannan ya samar da shugabanci mai ma'ana.

Tsohon gwamna daga arewa ya goyi bayan kiran neman Oshiomhole ya yi murabus
Oshiomhole
Asali: Depositphotos

"Makasudin kafa jam'iyya shine ta lashe zabuka, idan ta gaza yin hakan to babu amfanin jam'iyyar," a cewar Abdulkarim.

DUBA WANNAN: Sakkwatawa sun kaurace wa wurin rantsar da Tambuwal a Sokoto (Hotuna)

Ya kara da cewa Oshimhole ya karbi shugabancin APC a lokacin da take da gwamnonin jihohi 36, amma a karkashin shugabancinsa jam'iyyar ta rasa jihohin Adamawa, Oyo, Imo da Zamfara.

"Rasa jihohi har 6 ba kankanuwar asara ba ce ga mambobin jam'iyya. Idan Oshiomhloe bai sauka ba, APC zata karasa mutuwa a shekarar 2023," a cewar Abdulkarim.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel