Dankari: An kama wata mata dake kai wa fursinoni muggan kwayoyi a gidan yarin Kano

Dankari: An kama wata mata dake kai wa fursinoni muggan kwayoyi a gidan yarin Kano

- Jami’an hukumar da ke kula da gidajen yari na jihar Kano, sun yi ram da wata mata kan zargin kai wa fursunoni muggan kwayoyi

- An cafke matar ne a daidai lokacin da ta ke kokarin shiga gidan da wani kwali

- Da aka matsa da bincike sai aka gano cewa ashe kullin tabar wiwi ne har guda 39 a ciki

Rahotanni da ke zuwa mana daga jaridar Premium Times sun nuna cewa, jami’an hukumar da ke kula da gidajen yari na kasa babin jihar Kano, sun yi ram da wata mata mai suna Rifkatu Anthony bisa zargin kai wa fursunoni muggan kwayoyi.

An tattaro cewa an cafke Rifkatu ne a daidai lokacin da ta ke kokarin shiga gidan da wani kwali.

Da aka matsa da bincike sai aka gano cewa ashe kullin tabar wiwi ne har guda 39 a ciki zata shiga wa fursinonin da shi.

Dankari: An kama wata mata dake kai wa fursinoni muggan kwayoyi a gidan yarin Kano
Dankari: An kama wata mata dake kai wa fursinoni muggan kwayoyi a gidan yarin Kano
Asali: UGC

Ita dai Rifkatu ta ce sako ne zata kai ma wani a cikin gidan yarin. Tace wani mai suna ThankGod ne ya bata wannan kwali.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An shiga halin dar-dar a Jos yayinda hukumomin tsaro suka tura karin jami’ai

Shugaban hukumar reshen jihar Kano Gambo Abdullahi ya yabawa jami’an da suka kama wannan mata sannan ya kara da cewa hukumar ba za ta yi kasa-kasa ba wajen ganin ta rika kama irin wadannan mutane da ke shigo wa fursinoni kwayoyi cikin gidan yari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel