DSS: Wasu Masharranta ne su ka shirya mani mugun makirci - Malam Abu Ammar

DSS: Wasu Masharranta ne su ka shirya mani mugun makirci - Malam Abu Ammar

Ku na da labari cewa a kwanakin baya ne jami’an tsaro na DSS su ka damke wani Malamin addinin Musulunci mai suna wani Malamai mai suna Aminu Usman watau Abu Ammar a jihar Katsina.

An tsare wannan babban Malami ne bayan ya koka a kan yadda sha’anin tsaro ya tabarbare a jihar Katsina. Malamin ya bayyana cewa shi kadai ya ga irin abubuwan da ya gani a lokacin da ya ke hannun Jami’an DSS na kasar.

Malamin yake cewa ba wannan ne karon farko da aka kama shi ba, ya kuma ce wannan abu bai sa ya karaya ba. Ustaz Abu Ammar ya godewa irin addu’o’in da jama’a su ka rika yi masa inda yace wannan ne ya sa ya samu kubuta.

Wannan Malami ya fadawa ‘Dalibansa cewa wasu ne su ka shirya masa tuggu a wajen jami’an tsaro, ko da yake dai Malamin ya ki bayyanawa Almajiran na sa irin yadda ya sha ta-ta-burza da jami’an tsaron na DSS masu fararen kaya.

KU KARANTA: Malamin da aka damke a Bauchi yace DSS sun koya masa hankali

Abu Ammar yake cewa babu abin da zai ga bayan da’awar yadda Sunnah a Katsina da Najeriya ko da jami’an tsaro sun cafke sa. Malamin ya nemi jama’a su tsayawa gaskiya a kowane lokaci ba tare da goyon bayan wani mutum ba.

Shehin yake cewa dole yayi magana a kan irin kashe-kashen rayukan mutanen da ake yi a Garuruwan Batsari, Danmusa, Kankara, Sabuwa, Dandume, Faskari, Jibiya, Katsina, Mani, Daura da Batagarawa, har da kuma cikin Garin Katsina.

Malamin addinin musuluncin ya kuma nuna babu hannun gwamnatin jihar Katsina ko ta tarayya wajen daure sa da aka yi. Malam Abu Ammar yake cewa wasu ne su ka sa aka cafke sa inda yayi mumunan addu’a ga masu nemansa da sharri.

A jawabin Malamin lokacin da ya koma karatun tafsiri a makon jiya, yace babban burinsa shi ne a kawo karshen kashe-kashen mutanen da ake yi a Katsina kamar yadda ya bayyana a wata hudubar sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel