Kotu ta hana Gwamna Lalong kirkiro masarautu a Jos

Kotu ta hana Gwamna Lalong kirkiro masarautu a Jos

Wata babban kotun Jihar Filato, a ranar Alhamis ta bayar da umurnin dakatar da Gwamna Simon Lalong daga kirkiran wata sabuwar masarauta daga masarautar Gbong Gwom Jos.

Jastis Christine Dabup ya bayar da umurnin bayan sauraron lauyan wata kungiyar 'yan asalin Berom, Mr Niri Darong wadda ya shigar da gwamnatin jihar kara a kotu bisa yunkurin da tayi na kirkirar sabbin masarautu biyu daga masarautar ta Jos.

Kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito cewa gwamnatin jihar Filato da kirkiri masarautar Riyom da Jos ta Arewa daga hadadiyar masarautar Jos.

Kotu ta hana Gwamna Lalong kacaccala masarautar Gbong Gwom Jos
Kotu ta hana Gwamna Lalong kacaccala masarautar Gbong Gwom Jos
Asali: UGC

Kirkirar masarautun ya bar hadadiyar masarautar Jos da kananan hukumomi biyu kacal - Jos da Barkin Ladi a maimakon hudu a baya.

DUBA WANNAN: Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila

Gwamnatin Jihar ta kuma sanar da cewa Attah Aten na Ganawuri ne zai jagoranci masarautar Riyom yayin da Ujah na Anaguta zai jagoranci masarauatar Jos ta Arewa.

Kirkiran wannan masarautun bai yiwa wasu 'yan asalin Berom dadi ba hakan yasa mutanen karkashin jagorancin Mr Daniel Choji suka maka gwamnan jihar a Kotu domin dakatar da nadin sarautun.

Sunyi karar gwamnan jihar Filato da Alkalin Alkalan Jihar da kuma kwamishinan harkokin siyasa na jihar.

Saura da aka ambatta cikin takardan karar sun hada da shugaban karamar hukumar Jos ta Arewa da shugaban karamar hukumar Riyom.

Umurnin da alkalin kotun, Dabup ya bayar ya ce, "An haramtawa wadanda akayi kara daukan wata mataki da kacacala hadadiyar masarautar Jos ko kuma dakatarwa ko tsige wani mai rike da mukami har zuwa lokacin da aka zauna sauraron shari'ar."

Kotu ta zabi ranar 11 ga watan Yuni domin sauraron shari'ar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel