Kannywood: Ban durkusa domin bawa Nabruska hakuri ba - Hadiza Gabon
Jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta karyata cewa rundunar 'yan sanda na jihar Kano ta kama ta saboda ta ki amsa gayyatar kotu.
A hirar da Gabon tayi da Daily Trust a ranar Talata, ta ce babu gaskiya cikin labarin kuma wasu ne da ke son bata mata suna a idanun jama'a suka kirkiri labarin.
A baya, Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa jarumin Kannywood Mustapha Badamas Nabraska ya shigar da takwararsa Hadiza Gabon kara a wata kotun majistare inda ya ke zargin ta da cin zarafinsa.
A lokacin Alkalin kotu, Muntari Dandago ya bayar da umurnin kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, Mohammed Wakili ya kamo Gabon saboda kin amsa gayyatar kotu.
DUBA WANNAN: Manyan jaruman Kannywood uku sun samu wata babban kwangila
Amma Gabon ta ce, "Yan sanda ba su kama ni ba, rahoton karya ce tsantsagwaronta da aka kirkira domin a bata min suna.
"A halin yanzu da na ke magana, munyi sulhu da Nabraska da ya kai ni kotu. Saboda haka ban san inda aka samo labarin kama ni ba. Kotu ta janye umurnin tuntuni," inji ta.
Gabon wacce za ta cika shekaru 30 a duniya a watan Yuni ta kuma karyata labarain da wata kafar yada labarai ta wallafa na cewa ta durkusa ta nemi afuwar Nabraska sannan ya yafe mata ya janye karar.
Ta ce, "labarin karya ne, ban durkusa wa gaban sa ba (Nabraska); mun zauna ne mun tattauna mu kayi sulhu a wajen kotu."
Gabon wacce ta fito a fina-finan 'Jarumta', 'Gida da Waje' da 'Ciki da Raino' ta bukaci kafafen yada labarai su rika tabbatar da gaskiyar labari kafin su wallafa ta.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana
Asali: Legit.ng