Bincike ya nuna barnar da ake yi a Ma’aikatar sadarwar Najeriya

Bincike ya nuna barnar da ake yi a Ma’aikatar sadarwar Najeriya

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Ministan sadarwa na Najeriya Abduraheem Adebayo Shittu ya samu kan-sa cikin wata badakalar kwangiloli. Ministan dai yayi maza ya zare hannunsa daga zargin.

Bincike ya nuna cewa an tsula kudin aiki a mafi yawan kwangilolin da aka bada a ma’aikatar sadarwa daga farkon 2018 zuwa tsakiyar shekarar. Wasu kwangilolin ma dai an ci kudin su ne kurum.

Wannan bincike da Daily Trust tayi kwanan nan ya kuma tabbatar da cewa ma’aikatar sadarwar ta rika bada kwangiloli ne ga Abokai da ‘yanuwan manyan ma’aikatar a maimakon duba cancantar aiki.

Misali, wannan rahoto ya nuna yadda aka ba wani kamfani mai suna Delimit Nigeria Limited and SS Energy Nigeria Limited kwangilar wani aiki a Garin Ibadan a kan kudi Naira miliyan 300 kwanaki.

Bayan an karbi wannan kudi, ba ayi aikin ba. Wani daga cikin masu ba Ministan shawara a wancan lokaci, shi ya sa hannu aka biya kudin kwangilar, bayan an wawuri kudin, yayi murabus ya tsere.

KU KARANTA: Hukumar EFCC tana binciken Gwamna Okorocha - Magu

Bincike ya nuna barnar da ake yi a Ma’aikatar sadarwar Najeriya
Adebayo Shittu yana cikin wani zargi bayan badakalar NYSC
Asali: Facebook

Haka zalika akwai babban Darektan da ya sa hannu aka biya wani kamfani kudi har Naira Miliyan 90 domin yin wani kwangila a ma’aikatar amma har yau ba ayi aikin ba, kuma tuni an lashe kudin.

Akwai wani kamfani; Livial Soft Tech wanda aka jibgawa miliyoyin kudi domin shigo da wasu kaya. Har gobe babu labarin wannan kaya, kuma ana tunani Minista yana da alaka da masu wannan kamfanin.

Tun a 2017 ne aka ba kamfanin Livial Soft Tech Limited wannan kwangila da ake sa rai za a kammala cikin watanni 10, amma har yanzu da mu ke magana babu labarin wannan aiki a kasar inji jaridar.

Bugu da kari, akwai wasu miliyoyin kudi da ma’aikatar sadarwan tace ta kashe wajen horas da wasu ma’aikata. Amma har yanzu babu wanda ya san wani bayani a game da wanda aka kashewa kudin.

Wannan dogon rahoto ya nuna yadda aka rika bada wasu ayyuka na miliyoyin kudi da za ayi a Yankin Ogbomosho, Oyo, Nsukka, Enugu da Katsina ba tare da an bi sharudan raba kwangiloli ba.

Ma’aikatan kan hada kai ne da hukumar BPP wajen cin karen su babu babbaka inji jaridar ta Daily Trust. Sai dai Adebayor Shittu ya bayyana cewa sam bai da masaniya a kan wadannan tarin zargi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng