Wadanda za su tafi aikin Hajji ta Adamawa za su biya Miliyan 1, 510, 000

Wadanda za su tafi aikin Hajji ta Adamawa za su biya Miliyan 1, 510, 000

Mun ji labari Jaridar Daily Trust ta kasar nan ta rahoto cewa hukumar kula da aikin Hajji ta jihar Adamawa ta bayyana adadin kudin da za a biya a shekarar nan domin sauke farali a kasa mai tsarki.

Hukumar da ke kula da harkokin aikin Hajjin da jin dadin Alhazai na Adamawa ta bayyana cewa Mahajjatan da za su tashi ta jihar Adamawa, za su kashe Naira miliyan 1, 510, 000 ne a shekarar bana.

Babban Sakataren wannan hukuma, Malam Umar Bobboyi, shi ne ya bayyana wannan a Ranar Lahadi 19 ga Watan Mayun 2019. Bobboyi yayi wannan jawabi ne a cikin babban birnin Adamawa na Yola.

Boboyi yake cewa:

“Mun dauki wannan mataki ne domin sawakewa masu shirin sauke faran biyan kudin hajji.”

Umar Bobboyi yake cewa hukumar hajji ta Adamawa tayi wa jama’a rangwame bayan NAHCON sun kayyade kudin da za a biya a bana. Bobboyi yace sun rage fiye da N100 daga cikin kudin kujera a jihar.

“Bayan haka, Maniyyatan Adamawa su ne za su biya mafi karancin kudin kujera a bana…”

KU KARANTA: An bayyana kudin kujerun hajjin bana a Kaduna da Abuja

Malam Bobboyi yake cewa sun rage farashin ne domin Bayin Allah da ke da niyyar sauke-farali su ji dadin biyan wannan kudi. Sakataren yace wannan ya sa kujerun Adamawa su ka fi na ko ina araha.

Shugaban hukumar Alhazan ya kuma bayyana cewa an samu karin kusan N34, 000 daga abin da aka biya a shekarar bara. A karshe kuma yace an warewa jihar Adamawa kujeru 2, 601 a wannan karo.

Idan ba ku manta ba, A jiya kun ji cewa Hukumar Alhazan Jihar Kaduna ta yanke kudin kujerar Hajji na bana inda aka ji cewa Maniyyata za su kashe N1, 549,297.09 wajen sauke farali a kasa mai tsarki.

A karshen jawabin sakataren hukumar Alhazan yace:

“A wannan shekara kuma, an warewa jihar Adamawa kujerun har 2, 601 a kasa mai tsarki…”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel