Pantami, Muazu, Kauran Bauchi da Dogara sun taimake ni – Ustaz Abdulaziz

Pantami, Muazu, Kauran Bauchi da Dogara sun taimake ni – Ustaz Abdulaziz

Babban Malamin nan da aka kama a Garin Bauchi, Ustaz Idris Abdulaziz, ya bayyana yadda ta kaya da shi a hannun jami’an tsaro na DSS bayan an tsare sa a Birnin Abuja a makon da ya gabata.

Pantami, Muazu, Kauran Bauchi da Dogara sun taimake ni – Ustaz Abdulaziz
Malamin da aka damke yace ya koyi darasi bayan ya fito daga hannun DSS
Asali: Facebook

Malamin ya bayyana wannan ne a khutubar da yayi Ranar Juma’a. 17 ga Watan Mayu a masallacin sa da ke Dutsen Tanshi. Malamin yace ya koyi darasi a zaman kaso, wanda da bai taba samun irin sa ba.

Wannan Shehin Malamin ya godewa jama’a da su ka taimaka masa da addu’o’i a lokacin da yake tsare, inda ya kuma nuna farin-cikinsa a kan yadda Almajiransa su ka nuna dangana da wannan musiba.

KU KARANTA: A kan na caccaki Buhari aka aiko DSS su damke ni - Malami

Idris Abdulaziz yake cewa har Annabawa da Manyan Bayin Allah sun gamu da irin wannan jarrabawa na dauri a gidajen yari, inda yace zai cigaba da karatunsa yadda ya saba yi kafin a damke sa.

Ustaz Idris Abdulaziz ya fadi wasu daga cikin wadanda su ka taimaka wajen ganin an fito da shi bayan yayi mako guda a daure. Malamin yace daga ciki har da wadansu bai ko taba tunani ba.

KU KARANTA: NAHCON ta tabbatar kujerar Hajji ya kara tsada a shekarar bana

A cewar Malamin addinin, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya taimaka maso sosai, kuma har ya rika kawo masa ziyara a lokacin da ake tsare da shi. Malamin yace Pantami har shaida ya bada a kan sa.

Abdulaziz ya fadawa Almajiransa cewa tsohon gwamna Ahmad Adamu Muazu da gwamna mai jiran-gado Bala Mohammed, da sabon ‘dan majalisar Bauchi, Ibrahim Yakubu duk sun taimaka masa

Haka zalika kuma wannan Malami yake cewa shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ya taka rawar gani wajen fitowarsa. Malamin yace Minista Adamu Adamu shi me yayi bakin kokarinsa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel