An bayyana kudin kujerun hajjin bana a Kaduna da Abuja

An bayyana kudin kujerun hajjin bana a Kaduna da Abuja

Hukumomin Kula da Jin Dadin Alhazai na jihohin Kaduna da na babban birnin tarayya, Abuja sun bayyana cewa Naira Miliyan 1.5 ne kudin kujerar aikin hajjin bana da kowane maniyyaci zai biya a 2019.

Jami'an yadda labarai na hukumomin, Malam Yunusa Abdullahi da Muhammad Lawal sun bayyana hakan ne a cikin sanarwar da suka fitar a Kaduna da Abuja.

Sanarwar ta ce Cibiyar Kula da Aikin Hajji na Kasa ta amince da N1, 549,297.09 a matsayin kudin kujerar aikin hajji da kowane maniyyaci zai biya domin zuwa kasar Saudi Arabia sauke farali.

An bayyana kudin kujerun hajjin bana a Kaduna da Abuja
An bayyana kudin kujerun hajjin bana a Kaduna da Abuja
Asali: Depositphotos

Za kuma a bawa maniyyatan allawus din tafiya na $800.00.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta fitar da jawabi a kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin Buhari

Abdullahi na jihar Kaduna ya ce mai sanya idanu kan hukumar Alhazai na jihar, Imam Hussaini Ikara ya yi bayyanin cewa an cimma matsaya a kan kudin ne bayan anyin lissafi da kudin masauki a Makkah da Madina da sauran abubuwa.

"Ba a kayyade BTA ba kamar yadda akayi a shekarun baya.

"Mutanen da suka gudanar da aikin hajji a shekaru hudu da suka gabata za su biya kari Riyal 2000 wanda ya yi daidai na N162.000."

Sai dai Ikara ya shawarci maniyyata suyi gaggawan biyan kudin kejurun su domin tuni an fara aikin tantance biza kuma akwai bukatar a biya cikon kudin ga hukumar NAHCON kamar yadda aka tsara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel