'Yan bindiga sun sace mutane 8 a Zamfara, sun nemi N50m

'Yan bindiga sun sace mutane 8 a Zamfara, sun nemi N50m

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kara sace wasu mutane 8 a garin Kanoma dake karkashin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Da yake bayar da bayani a kan faruwar lamarin, wani mazaunin garin Kanoma, Alhaji Ibrahim Kanoma, ya ce 'yan bindigar sun dira a garin da misalin karfe 1:00 na daren ranar Litinin tare da yin harbin iska domin firgita jama'a.

Ibrahim ya bayyana cewar 'yan bindigar sun sace mutane 24 ne amma daga baya suka sako 16 daga cikin su, "saboda sun gan su a wahale", sannan suka yi awon gaba da ragowar mutane 8.

A cewar sa, bayan musayar kiran waya, 'yan bindigar sun nemi a basu miliyan N50m kafin su saki mutanen.

'Yan bindiga sun sace mutane 8 a Zamfara, sun nemi N50m

'Yan bindiga sun sace mutane 8 a Zamfara, sun nemi N50m
Source: Facebook

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ta wayar tarho, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Zamfara, ASP Mohammed Shehu, ya ce an sace mutanen ne a garin Kanoma da misalin karfe 1:00 na daren ranar Litinin.

Kakakin ya ce rundunar 'yan sanda ta gaggauta tura jami'anta, bayan ta samu labari, domin su ceto mutanen da aka sace.

DUBA WANNAN: An kama 'yan Boko Haram 4 da suka gudu zuwa jihar Edo

Wani sanannen malamin addini a garin, Sheikh Ahmad Umar Kanoma, ya yi kira ga hukumomin dake da ruwa da tsaki da su gaggauta daukan matakan kubutar da mutanen da aka sace tare da yin kira ga gwamnati da ta kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi jihar Zamfara.

Da yake magana a kan matsalar 'yan bindiga a Zamfara yayin tafsirin watan Ramadana, Sheikh Kanoma, ya ce akwai babban hatsari a nan gaba matukar ba a dauki matakan gaggawa domin kawo karshen abin a yanzu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel