Sojoji sun aike da 'yan Boko Haram 7 lahira, sun kwato bindigu, hotuna

Sojoji sun aike da 'yan Boko Haram 7 lahira, sun kwato bindigu, hotuna

Rundunar sojin Najeriya ta 7 Division ta ce dakarunta na atisayen 'HARD STRIKE' tare da hadin gwiwar da 'yan sa kai na Civilian JTF sun kai samame a ranar Alhamis, 10 ga watan Mayun 2019 a kauyukan Fuye da Melere da ke jihar Borno inda suka yi artabu da wasu 'yan Boko Haram a Gulwa.

Sagir Musa, direktan yada labarai da hulda da jama'a na NA ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabai da ya fitar a ranar Juma'a.

"Sojojin sunyi nasarar halaka 'yan ta'adda bakwai tare da kwato bindigu kirar AK 47 guda 6 da kuma FN Rifle guda daya.

Dakarun sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 7, sun kwato bindigu

Dakarun sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 7, sun kwato bindigu
Source: Twitter

Dakarun sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 7, sun kwato bindigu

Dakarun sojoji sun kashe 'yan Boko Haram 7, sun kwato bindigu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An tura 'zauna gari banza' gidan yari saboda taba nonon kwaila

"Babu wani soja ko jami'in tsaro da ya rasa ransa sakamakon artabun da akayi da 'yan ta'addan," inji Musa.

Musa ya ce dakarun sojin za su cigaba ba za suyi kasa a gwiwa ba har sai sunga bayan ta'addanci da sauran laifuka tayar da zaune tsaye a Najeriya.

Ya kuma ce za su cigaba da wayar da kan jama'a tare da neman bayyanai masu amfani da za su taimakawa rundunar sojin wurin yakin da ta keyi da ta'adddanci domin magance kalluballen tsaro da ke fama da shi a sassan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Online view pixel