Kirkirar sabbin masarautu: Mutanen Kano ba za su lamunta ba - Naniya

Kirkirar sabbin masarautu: Mutanen Kano ba za su lamunta ba - Naniya

Wani fitaccen masanin tarihi a Jami'ar Bayero ta Kano, Dokta Tijjani Naniya ya ce al'ummar jihar Kano ba za su amiince da yunkurin da gwamnatin jihar keyi na kokarin jefa masarautar Kano a cikin ruguntsimin siyasa ba.

Masanin ya yi wannan jawabin ne yayin mayar da martani a kan ikirarin da aka ce gwamnatin jihar za tayi na rage karfin mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ta hanyar kirkirar wasu masaurautu hudu a Karaye, Bichi, Rano da Gaya.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa wasu na kusa da gwamnan sun ce akwai kulalliya tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da Sarkin na Kano sakamakon ikirarin da akayi na cewa Sarkin ya goyi bayan dan takarar gwamna na PDP, Abba Yusuf a zaben da ta gabata.

Kirkirar sabbin masarautu: Mutanen Kano ba za su lamunta ba - Naniya
Kirkirar sabbin masarautu: Mutanen Kano ba za su lamunta ba - Naniya
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: Shugaba Buhari ya hallarci bude Tafsirin watan Ramadan, hotuna

Sai dai a wata hira da akayi da Mr Naniya a gidan rediyon Freedom a ranar Talata, ya nuna rashin jin dadin sa kan yadda wasu 'yan siyasa ke yunkurin yin katsalandan cikin harkokin masarautar.

Ya ce yunkurin na kirkirar sabbin masarautu a Kano ba abu ne mai kyau ba kuma hakan zai sanya sauran kasashen duniya su mayar da Kano abin dariya.

Ya cigaba da cewa tarihi ya nuna cewa kimanin shekaru 800 da suka shude, masarautun Rano, Gaya, Bichi da Karaye sun amince da yiwa masarautar Kano biyaya bayan an ci su da yaki a wannan lokacin.

"Tun wannan lokacin wadannan masarautun suna karkashin masarautar Kano ne. Kazalika, masarautar Kano ce ta nadi sarakunan da suka mulki wadannan masarautun. An zabi sarakunnan ne daga cikin wadanda suka yi jihadi a wannan lokacin.

"Tarihi ya nuna cewa masarautar Kano ba ta amince da katsalandan. Anyi yunkurin rage karfin masarautar a 1980 da 1981 amma hakan bai haifar da da mai idanu ba a wannan lokacin.

"Abin takaici ne yadda aka wofinta da kusan dukkan al'addun mu na gargajiya, sarakunan gargajiyan mu sune kadai abinda ya rage da 'yan siyasa ba su lalata ba. Ba zamu amince da hakan ba. Ba za ta yiwu ba.

"Masarautar Kano itace abinda ya rage da muke alfahari da ita saboda haka duk wata yunkuri da za ayi na kawo mata cikas ba zai yiwu ba," inji Naniya.

Tsohon kwamishinan ya kuma ce bai ga dalilin kirkirar masarautun ba duba da cewa tsaffin masarautun ba su koka da cewa masarautar Kano na nuna musu wariyya ko fin karfi ba.

Ya yi gargadin cewa yunkurin da wasu 'yan siyasa ke yi na kawo cikas ga masarautar Kano ba za zai haifar da alheri ba.

Legit.ng ta kawo muku cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya nemi amincewar majalisar dokoki na jihar su bashi damar kirkirar sabbin masarautu a jihar.

A zaman majalisar na ranar Litinin, Kakakin majalisar, Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya karanto wata wasika dauke da sa hannun wani Ibrahim Salisu da wasu da ke neman kirkirar masarautu a Karaye, Rano, Gaya da Bichi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel